Rayuwar da Boko Haram ta rusa kafin a ceto ta

Matar da Boko Haram ta ceto
Bayanan hoto, Zulaihatu 'yar asalin Adamawa ce amma tsananin damuwa ya jefa ta cikin rayuwar wahala inda ta tafi Kano da Sakkwato don gujewa bakin ciki

Rikicin Boko Haram a Najeriya da sauran kasashen yankin Tafkin Chadi ya yi sanadin tarwatsa garuruwa da birane musamman a yankin arewa maso gabashin kasar inda tarzomar ta fi kamari.

Alkaluma na cewa fiye da mutum miliyan biyu da dubu 400 ne suka tsere daga gidajensu, ciki har da mutanen da hare-hare suka tilas musu tserewa kimanin miliyan biyu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Rikicin Boko Haram a yanzu yana kara lafawa, a lokaci guda kuma dakarun tsaro na ci gaba da samun galaba kan mayakan kungiyar a arewa maso gabashin, ko da yake har yanzu sukan kai hare-hare.

Sai dai, wani abu da ba a cika mayar da hankali kansa ba, shi ne halin dimauta da zautuwa da matan da rikicin ya yi sanadin mutuwa ko batan mazaje da 'yan'uwansu kan shiga.

Zulaihatu Sani, 'yar jihar Adamawa ce da ta yi gudun hijira har zuwa jihar Sakkwato, kuma hare-haren da suka yi sanadin kashe mata miji da mahaifi tare da yayyenta uku sun yi matukar dimauta ta tsawon shekara.

Ta kwashe shekaru kusan hudu tana gararamba daga wannan unguwa zuwa waccan cikin halin dimauta tare da danta mai suna Buhari.

"Ina aure (a garin) Mubi (sai) aka kashe min maigida, sai na taho gida, (bayan) sati biyu sai anka shigo garinmu aka kashe min babana. Yanzu uwata ban san inda take ba, in ji Zulaihatu.

Ta kara da cewa: "Da ciki na taho garin ga, na shigo nan."

Ba dai iyakar tashin hankalin da Zulaihatu ta gani kenan ba, domin bayan ta gudu daga jihar Adamawa zuwa kano, sai aka kai kazamin hari kan babban masallacin birnin Kano da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 a shekara ta 2014 abin ya tilasta mata kara nausawa yamma zuwa Sakkwato.

Short presentational grey line

Zulaihatu ta ce ta rika kwana a babbar tasha tsawon lokaci, kafin daga bisani ta koma wata unguwa, daga nan kuma ta koma Binji Pharmacy da kwana.

Kungiyar Asatahir Foundation ce ta ga wannan mata tana gararamba a kan titi da rumfar kasuwa inda take kwana, don haka ta yanke shawarar tallafa wa Zulaihatu.

Boko Haram after Attack

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin Boko Haram ya daidaita mutane da dama daga muhallansu kuma ya rarraba iyalai

Shugaban kungiyar Aliyu Sidi Attahiru hankalinsu ya tashi ganin Zulaihatu na gararamba taro da dan karamin yaro a kan titi, "Za ka gan ta wurin rumfar mai nama tana kwance, wani lokaci ka gan ta bakin wani shago."

Ya ce kungiyar na aikin ciyar da gomman masu rangwamen gata a kullum, kuma Zulaihatu kan je don ta karbi irin wannan tallafin abinci, amma sai wasu suka ga cewar matar na bukatar tallafin da ya fi na abinci.

"Yanzu lokaci ya lalace, wasu za su iya yi mata fyade, wasu za su iya dauke danta.

"Sai muka tattauna da mutanen unguwa, kuma wurin da aka ba mu (don mu sauke ta), muka je muka gyara mata, muka sa mata katifa, muka ja mata wutar lantarki, muka sa mata fanka" in ji Aliyu Sidi.

Ya kara da cewa: "Kuma muka ga ai shi danta dan shekara hudu ne zuwa biyar, (don haka) muka sa shi makaranta, muka sai ma shi yunifom. Komai ake sai ma shi, mu ne muke daukar takalihin shi na karatu."

A cewarsa hatta ga batun kula da lafiya, kungiyar Asatahir ta yi rijista da wani babban kamfanin magani don ya rika ba ta magani idan an rubuto mata a asibiti a duk lokacin da ta gamu da larura.

Sai dai a bayyane take cewa akwai mata da yara daruruwa ko ma dubbai da ke cikin irin wannan halin, amma ba su yi katarin samun irin wannan tallafin ba da Zulaihatu da kuma danta suka samu, abin ke da nuna girman bukatar gwamnatoci da kungiyoyi da ma daidaikun jama'a su kawo wa irin wadannan mutanen dauki wajen sake gina sabuwar rayuwa.