Hotunan yadda 'yan gudun hijira ke rayuwa a Zamfara

'Yan gudun hijirar da ke ci gaba da kauracewa gidajensu a kauyukan Zamfara na cikin mawuyacin hali da bukatar agajin gaggawa.

'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Kusan mutune dubu ashirin suka kauracewa muhallansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga a Zamfara
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Gwamnati ta ce kauyuka kusan 20 ne jama'arsu suka yi kaura a karamar hukumar Zurmi kadai.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Mutanen sun watse a kauyukan da ke mazabu uku wato Mashema da Birane da kuma kwashabawa a karamar hukumar mulki ta Zurmi.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Yawancin 'yan gudun hijirar na kwarara daga Kauyukansu zuwa garin Zurmi.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Wasu suna rayuwa ne a asibiti, wasu kuma a makarantun boko na firamare.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Mutanen kauyukan na gudun hijira tare da dabbobinsu.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Yawancinsu an kashe mazajensu da matansu, yayin da yara suka koma marayu.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, An shafe tsawon shekaru takwas ana fama da matsalar tsaro a jihar Zamfara
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Duk da gwamnatin jiha da ta tarayya na ikirarin suna iya kokarinsu amma al'ummar wadannan yanki na Zamfara na kokawa da rashin kai dauki da kuma taimakon gaggawa.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Wasu alkalumma sun ce tsakanin mako biyu an kashe mutum kusan 150 a Zamfara, dalilin da ya tilastawa mutane gudun hijira saboda tsoron hare-hare.
'Yan gudun hijirar rikicin Zamfara

Asalin hoton, Abdulrazak Bello Kaura

Bayanan hoto, Akwai dai bukatar samar da tallafin gaggawa da kyakkyawan tsaro ga 'Yan gudun hijirar na Zamfara.