Fafaroma ya bai wa 'yan gudun hijira tallafin dala 500,000

Fafaroma Francis ya bayar da tallafin dalar Amurka dubu 500 kimanin kudin Najeriya miliyan 180 ga 'yan gudun hijira.

An bayyana cewa kudin za su amfani 'yan gudun hijiran da suke gararamba ko kuma suka rasa mafaka a Mexico a kokarin da suke yi na tsallake iyakar Amurka.

An dai samu kudin ne daga asusun cocin Katolika na ''Catholic Church's Peter's Pence fund'' bayan sauran coci-coci na duniya sun tattaro gudummawarsu.

A kwanakin baya dai Fafaroman ya caccaki shugaban Amurka Donald Trump sakamakon kudirinsa na kokarin gina katanga domin hana kwararar 'yan gudun hijira.

Gwamnatin Amurka dai ta matsa lamba ga gwamnatin Mexico da ta magance matsalar ayarin mutanen da ke kwararowa daga Amurka ta tsakiya suna daukar hanya zuwa Arewaci.

A 2018, ayarin mutum shida ne suka shiga Mexico da suka kai mutum dubu 75 kamar yadda ofishin Cocin Katolika na Peter's Pence da ke kula da bada tallafin ya bayyana.

Da dama daga cikin masu gudun hijira na gudu ne sakamakon gudun rikici da talauci da kuma azabtarwa a kasashensu.

A makon da ya gabata an bayyana cewa a kalla 'yan gudun hijira 400 aka kama ya yin da suke ratsawa ta cikin Mexico za su tafi Amurka.

Ofishin na Peter's Pence ya bayyana cewa kafafen yada labarai sun rage kawo rahotanni da labarai kan irin wadannan abubuwan wanda hakan ya yi sanadiyar rage samun tallafi daga gwamnatoci da kuma kungiyoyi da jama'a masu zaman kansu.