Ra'ayoyin 'Yan Gudun Hijira a Borno

A daidai lokacin da ya rage kwanaki biyu kawai a gudaanar da babban zabe a Najeriya da dama daga cikin wasu 'yan gudun hijira da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri sun sanar da cewa a shirye suke su jefa kuri'arsu a ranar zaben domin sauke nauyin da ya rataya a kansu.

Wakilin BBC Abdou Halilou da yanzu haka ya ke a garin na Maiduguri ya zagaya daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijirar. A sha saurare lafiya.