Ba hutu na je yi Landan ba – Buhari

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar Alhamis ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Landan, a wata ziyara da fadarsa tace ta kashin kai ce.

Wata sanarwa da fadar shuganban kasar ta fitar ta ce Shugaba Buhari zai shafe kwana 10 a Landan kafin ya koma Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya ce shugaban zai ringa gudanar da aiki daga can, domin kuwa ba hutu ya tafi yi ba.

Tuni dai Shugaba Buhari ya isa Landan din, inda wasu hotuna da mai ba shi shawara kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ya wallafa a Twitter, suka nuna lokacin da shugaban ya isa Landan din.

Tafiyar shugaban dai ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya inda suka rika bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Twitter.

Mutane da dama na ganin cewa shugaban ya je ganin likitoci ne kamar yadda ya saba, amma fadarsa ta musanta hakan.

Mallam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa ziyarar tafiya ce ta kwana 10 ce don gudanar da wasu harkokin kashin kansa da ba su shafi aikin ofis ba.

Sai dai da alama wasu 'yan Najerya ba su gamsu da bayanin Malam Garba Shehu ba.

Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna Super Ceeto ya ce: "Neman magani a kasar waje ya zama tafiya ta kashin kai? Ko kuwa ba mu da hakkin sanin abin da shugabanmu ya je yi a Landan?"

BBC ta tambayi Garba Shehu ko takamaimai tafiyar ta mece ce? Sai ya ce da wuya shugaban Najeriya ya shafe tsawon kwana 10 a duk inda yake ba tare da an ji duriyarsa ba.

Don haka: "In dai aka yi hakuri, za a gani. Kuma ba abubuwa ne da za a boyewa jama'a ba".

Ya ce ba sa fata wata larura ta kai Muhammadu Buhari ganin likita a wannan ziyara tasa.

A cewarsa: "Mu a saninmu, Shugaba Buhari, Allah ya ba shi cikakkiyar lafiya. Kuma idan akwai bukatar zuwa asibiti, ai babu dalilin sakayawa 'yan Najeriya."

Wasu 'yan Najeriya kuwa sun mayar da tafiyar shugaban abin barkwanci.

Ameer Mu'azu wani mai amfani da shafin Twitter ya wallafa sako ne kamar haka: "Da safe: Legas, Da Rana: Maiduguri, Da Dare: Landan" sannan ya yi wa shugaban kirari ta hanyar yi masa lakabi da 'Kyaftin' wato matukin jirgin sama kuma ya kare bayanin nasa da hoton zolaya 'emoji' na matukin jirgi.

A shekarar 2017, Shugaba Buhari ya yi jinya tsawon kusan wata 3 a birnin na Landan inda ba a san takamaimai ciwon da ya yi ba, kuma ko a wancan lokacin 'yan Najeriya sun yi ta tofa albarkacin bakinsu dangane da zamansa a Burtaniya.