Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari zai koma London ganin likita
A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin London domin duba lafiyarsa.
Wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta ce Shugaba Buhari zai shafe kwaki hudu likitocinsa suna duba shi.
An fitar da sanarwar ne ranar Litinin da daddare, kwana guda gabanin tafiyar shugaban zuwa London.
Malam Garba Shehu ya ce ko a makon da ya gabata ma Shugaba Buhari ya ga likitansa, lokacin da jirginsa ya yi ratse a kan hanyarsa ta komawa Najeriya bayan kammala ziyarar aiki a Amurka.
Kakakin na shugaban kasa ya ce a lokacin ne, likitan ya ce akwai bukatar sake duba lafiyarsa, inda kuma shugaban ya amince.
Tuni dai aka dage ziyarar aiki ta kwanaki biyu da aka tsara Buhari zai kai jihar Jigawa, inda yanzu ake sa ran kai ziyarar bayan ya koma Najeriya ranar Asabar, kamar yadda Garba Shehu ya bayyana.
Yada zangon da Buhari ya yi a birnin London a makon jiya ya janyo ce-ce-ku-ce da tambayoyi daga 'yan kasar da dama.
Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ma ta fitar da sanarwa tana neman lallai a yi karin bayani kan dalilin da ya sa Buhari zuwa London, duk kuwa da hakan ba ya cikin tsarin tafiyarsa.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
- 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
- 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
- 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
- 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
- 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
- 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
- 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
- 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
- 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
- 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a Landan
- 23 ga watan Yuli - Ya gana da wasu gwamnoni
- 26 ga watan Yuli - Ya sake ganawa da wasu karin gwamnoni
A bara Shugaban Najeriya ya shafe kusan wata biyu yana jiya a birnin London, ta cutar da ba a bayyanawa 'yan kasar ainihin abinda ke damunsa ba.
Batun rashin lafiyar shugaban ya janyo tsaiko wajen tafi da al'amuran gwamnati da dama a kasar.
Wasu 'yan kasar sun yi ta zanga-zanga kan cewa idan shugaban ba zai iya mulki ba to ya sauka, ya mikawa mataimakinsa ragama.
A watan jiya ne Shugaba Biuhari ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2019.