Indiya da Pakistan na gwabza yaki a sararin samaniyar Kashmir

Pakistan soldiers by what Pakistan says is a downed Indian jet

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 6

Jiragen yakin Indiya da Pakistan na gwabza yaki a sararan samaniyar Kashmir, a wani sabon rikici da ke neman kazanta tsakanin kasashen biyu.

Gwamnatin Pakistan ta ce ta kai hare-hare ta sama a matsayin martani kan makwabciyarta, ta kuma harbo jiragen saman Indiya guda biyu, da kuma cafke matukan jirgen.

Sai dai Indiya ta ce jirginta guda kawai aka kakkabo, kuma ita ma ta harbo wani jirgin Pakistan mai saukar ungulu. Haka nan kuma ta ce ta murkushe kokarin Pakistan na kai hari akan sansanin dakarunta.

Firai Ministan Pakistan, Imran Khan ya yi gargadi halin da wannan rikici ka iya jefa bangarorin biyu inda ya bukaci a shiga tattaunawar fahimtar juna.

Tun bayan samun 'yancin kansu dai a 1947, kasashen sun yi fada da juna ya kai sau uku. Biyu daga cikin yakin duk an yi ne kan Kashmir.

Hare-haren saman da ake yi a tsakanin yankin da ya raba inda Indiya da Pakistan ke da iko, su ne irin su na farko tun bayan wani yaki a 1971.

Sun biyo bayan wani harin mayakan sa kai ne da aka kai Kashmir wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 40 daga cikin dakarun Indiya - wanda shi ne mafi muni da ya faru cikin shekara 30 na yaki da ake yi kan mulkin da Indiya ke yi a Kashmir.

Wata kungiya mai cibiya a Pakistan ta ce ita ta kai harin.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wakilin BBC a Delhi Soutik Biswas, ya ce a yanzu kalubalen da ke gaban Indiya da Pakistan shi ne yadda za a shawo kan wannan tashin hankalin na baya-baya, kafin abubuwa su sake munana.

Me muka sani game da lamarin?

Mai magana da yawun rundunar sojin Pakistan ya ce matukin jirgin Indiya daya ne kawai a hannunsu. Da fari jami'ai sun ce matuka jirgi biyu aka kama kuma an kai dayansu asibiti.

Ba a bayar da wani bayani kan abun da ya sa adadin ya sauya ba.

Manjo Janar Asif Ghafoor ya ce ana kula da Wing Commander Abhinandan ne saboda "bin doka irin ta soji."

Da fari ma'aikatar yada labarai ta Pakistan ta wallafa wani bidiyo wanda daga bisani suka goge - da ke nuna matukin jirgin an rufe masa ido - yana kuma bayyana kansa ga sojoji.

Image purportedly showing captured Indian pilot

Asalin hoton, Pakistan Information Ministry

Bayanan hoto, Ma'aikatar yada labarai ta Pakistan ta wallafa wani bidiyo wanda daga bisani suka goge - da ke nuna matukin jirgin an rufe masa ido - yana kuma bayyana kansa ga sojoji

Wani bidiyon kuma da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda 'yan Pakistan mazauna Kashmir ke dukan matukin jirgin kafin isowar sojojin Pakistan.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Presentational white space

A Indiya kuwa, ma'aikatar harkokin waje Raveesh Kumar ya tabbatar da cewa an harbo jirgin kuma matukinsa ya mutu.

Ya kuma ce wani jirgin Indiya ya harbo wani jirgin yakin Pakistan kuma dakarun Indiya sun ga lokacin da ya fado a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan. Pakistan dai ta musanta cewa an harbo wani jirginta.

Daga bisani ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta fitar da sanarwa inda take bukatar a saki matukin jirgin yakinta ta kuma yi Allah wadai da hotunan Wing Commander Abhinandan da Pakistan ta fitar, tana mai bayyana su da cewa "wulakanta sojan da ya ji rauni ne."

Wanne irin martani Indiya da Pakistan ke mayarwa?

A wani jawabi da ya gabatar a gidan talbijin, Firai Minista Khan ya yi wa Indiya tayin tattaunawa kan ta'addanci da kuma gargadin kan tabarbarewar lamarin.

"Idan muka bari ya faru, to abun zai fi karfinmu daga ni har Narendra Modi," in ji shi.

"Abun da muke yi shi ne kawai mu sanar musu cewa kamar yadda suka kutsa mana iyakarmu, to mu ma fa za mu iya kutsawa iyakarsu," ya kara da cewa.

Har yanzu Mista Modi bai yi tsokaci kam lamarin ba, sai dai yana ganawa da manyan jami'an tsaro da na leken asiri don tattauna lamarin, kamar yadda rahotannin Indiya ke cewa.

Minsitan harkokin wajen Indiya Sushma Swaraj ta ce kasarta za ta dauki matakin "cikin nutsuwa da kulawa."

"Indiya ba ta fatan lamarin ya kara tabarbarewa," kamar yadda ta fada a lokacin da taje magana da ministocin tsaron Rasha da China.

Me ya faru lokacin hare-haren sama na farkon?

Tabcacin da Pakistan ta bayar na cewa ta harbo jiragen yakin Indiya biyu ya zo ne jim kadan bayan da Islamabad ta ce jiragen yakinta sun makale a yankin da Indiya ke iko da shi.

Hukumomin Indiya sun ce an tilastawa jiragen yakin Pakistan janyewa.

Mai magana da yawun rundunar sojin Pakistan Manjo Janar Ghafoor ya ce jiragen yakin sun kai hari wurare shida a yankin Indiya amma kuma daga baya harin ya sauka ne a filin Allah Ta'ala.

Ya ce: "Ba ma so mu shiga yaki."

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Presentational white space

India ta ce hare-haren na ranar Talata a Balakot, arewa maso yammacin Pakistan ya hallaka mayakan sa kai da dama, amma kasar ta ce ba a samu asarar rayuka ba.

Amurka da EU da China duk sun yi kira da a dakatar da fadan.

Presentational grey line

'Kalubale'

Soutik Biswas, BBC News, Delhi

Kalubalen da a yanzu ke gaban Indiya da Pakistan shi ne yadda za a shawo kan lamarin kafin abubuwa su tabarbare.

Ana ganin kamar abun da ke faruwa ga kasashen biyu masu karfin nukiliya na kai wa juna hare-haren abu ne da kusan bai taba faruwa ba a baya.

"Mun shiga yanayi na hatsaniya," in ji Husain Haqqani, tsohon jakadan Pakistani a Amurka kuma mai bai wa shugabannin Pakistan uku na baya shawarwa, ya shaida min ranar Talata da daddare.

Wani mai sharhi kan al'amuran tsaro na Indiya ya yi amanna cewa dakarun tsaron Indiya a yanzu za su shirya don tunkarar "duk wani rikici da ka iya tasowa.

Presentational grey line

Me yake faruwa?

Pakistan ta rufe kan iyakarta ta sararin samaniya, kamar yadda hukumar kula da sararin samaniyar kasa ta fada.

Rahotanni sun ce an rufe filayen jiragen sama guda tara na Indiya na wucin gadi amma a yanzu an sake bude su.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Presentational white space

Wata hukuma mai kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ce jiragen kasashen duniya su kaucewa bi ta yankin.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Presentational white space

Dakarun Indiya da na Pakistan duk suna ta ruwan bama-bamai a yankin Kashmir da ke karkashin ikonsu. An kashe fararen hula hudu na Pakistan kuma mutum 10 sun ji rauni a ba-ta-kashin da aka yi a kan iyakokin ranar Talata.

A daya bangaren, sojojin Indiya biyar ne suka jikkata kamar yadda jami'ai suka shaida wa BBC. An rufe wasu makarantu da ke yankin.

An kuma umarci mutanen da gidajensu ke kusa da kan iyakokin da su bar wajen.

A wani lamarin daban kuma ranar Laraba da safe, mutum shida daga dakarun sojin saman Indiya sun rasa rayukansu yayin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hatsari a Kashmir.

Ma'aikatar tsaro ta Indiya ta ce lamarin ya faru ne yayin wani atisaye da aka saba yi, kuma hatsari ne ya faru.

Map of region
Grey line

Hare-haren Indiya da Pakistan a takaice

Bayanan bidiyo, A watan Disamba Yogita Limaye ta fayyace yadda ake samun karuwar tashin hankali a Kashmir

Oktobar 1947: Yakin farko tsakanin Indiya da Pakistan kan Kashmir watanni biyu kawai bayan da suka samu 'yancin kai.

Agustan 1965: Makwabtan junan sun sake yin fada a kan Kashmir.

Disambar 1971: Indiya ta goyi bayan yankin Gabashin Pakistan kan muradinta na samun 'yancin kai. The Indian air force conducts bombing raids inside Pakistan. The war ends with the creation of Bangladesh.

Mayu 1999: Sojojin Pakistani sun mamaye wuraren da sojojin Indiya suke a tsaunukan Kargil mountains. Indiya ta kaddamar da hare-hare ta sama da kasa, kuma ta fatattaki wancan bangare.

Oktobar 2001: A kai wani mummunan hari majalisar dokoki da ke yankin Kashmir da ke karkshin ikon Indiya inda mutum 38 suka mutu. Wata biyu bayan nan, aka kai wani harin Majalisar Dokokin Indiya da ke Delhi har mutum 14 suka mutu.

Nuwambar 2008: An kai wasu hare-hare da aka kitsa a babbar tashar jirgin kasa ta Mumbai da wasu manyan otal-otal da kuma cibiyar Yahudawa inda mutum 166 suka mutu. Indiya ta zargi wata kungiya mai cibiya a Pakistan Lashkar-e-Taiba da hakan.

Janairun 2016: Wani hari da aka yi kwana hudu a jere ana kai wa kan sansanin sojin sama na Indiya a Pathankot ya hallaka sojojin kasar bakwai da kuma mayakan sa kai shida.

18 Satumbar 2016: Harin da aka kai sansanin soji da ke Uri a yankin KAshmir na Indiya ya hallaka mutum 19.

30 ga Satumbar 2016: Indiya ta ce ta kai wasu hare-hare kan mayakan sa kai ayankin Kashmir na Pakistan. Amma Pakistan ta musanta cewa an kai mata harin.