Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Brexit: Daftarin Therasa May ya sha kaye a majalisa
Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk ya shawarci Burtaniya ta ci gaba da zama a cikin kungiyar, bayan majalisar kasar ta yi fatali da daftarin firaminista Theresa May na ficewa daga Turai.
A wani sako twitter da ya wallafa mista Tusk ya ce idan yarjejeniya taki samuwa, kuma babu wanda ya ke son ganin an cimma daidaituwa, to wane ne ya ke da zuciyar cewa ga shawara takamaimai.
'Yan majalisa 432 ne suka jefa kuri'a kin amincewa da daftarin, yayin da 202 suka yi na'am dashi. Tuni dai Jami'ai a Turai da 'yan siyasa suka soma nuna rashin jindadinsu da sakamakon.
Wannan ya kasance gagarumin kaye irinsa mafi girma da wata gwamnatin Burtaniya mai ci ke fuskanta a tarihi, inda kuri'u 118 na adawa ya fito daga bangaren jam'iyyar Conservative ta firaminista Theresa May.
Sakamakon zaben ya haifar da kokwanto a zukatan masu fatan ganin lallai Burtaniya ta raba gari da Tarayyar Turai, kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya bijiro da batun jefa kuri'ar yanke kauna ga gwamnatin Misis May.
Hakazalika sakon twitter Mista Tusk, na cigaba da jan hankali yayin da wasu ke tafka muhawara kan mokar kasar a sassan Turai.
A nashi martanin shugaban hukumar tarayyar Turai Jean Claude Juncker ya gargadi cewa lokaci na kurewa Burtaniya na iya cimma wata yarjejeniyar.
Shi kuwa Babban jami'in da ke shiga tsakanin na kungiyar Tarayyar Turai kan ficewar Burtaniyar daga kungiyar, Michel Barnier ya ce lokaci ne da ya kamata gwamnatin Burtaniya ta fito ta bayyana takamaiman matakin da za ta dauka, domin kawunan kungiyar zai cigaba da kasancewa a hade da jajircewa wajen neman daidaituwa.
Tuni dai suma kasashen Jamus da Faransa da Ireland suka mayar da martanin nuna rashin jindadinsu tare da fargabar yanayin da turai za ta iya tsintar kanta muddin abubuwa suka gaggara daidaituwa.