Atiku ya kaddamar da shirin 'ceto Najeriya daga kangi'
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da manufofinsa na "ceto' kasar daga mawuyacin halin da take ciki.
Atiku - wanda ya bayyana manufofinsa a wajabin da ya gabatar kai-tsaye a shafin Facebook - ya kara da cewa babban burinsa shi ne ya samawar "matasan Najeriya nagartaccen ilimi wanda babu irinsa a duniya."
"Shirye-shiryena za su karfafa mata, su rage yawan mutuwa lokacin haihuwa da kuma dogaro da kai," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ya kara da cewa a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa ya jagoranci majalisar tattalin arzikin gwamnatin Najeriya wacce ta "samar da kudin shiga mafi tsoka da kuma kashi shida na arzikin da kasa ke samarwa a shekara irin sa na farko a kasar."
"Mun kaddamar da shirin wayoyin GSM wanda ya sa kasar ta tashi daga mai layin wayoyin salula 100,000 zuwa miliyan 100 a yau.
"Mun samu wannan nasara ne saboda mun yi tsari mai kyau."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Atiku Abubakar ya ce tambaya mafi muhimmanci da 'yan kasar suka kamata su yi wa kansu lokacin zabe ita ce: "Shin shekara hudu da suka wuce zuwa yanzu, wanne lokaci kuka fi jin dadi?
"Mun samu karin arziki ko kuwa mun talauce?"
A cewarsa, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai mayar da hankali wajen gayyato masu zuba jari da kuma tallafawa kananan sana'o'i fiye da miliyan 50 a duk fadin Najeriya domin su nunka arzikin da kasar ke samu su kai dala 900 zuwa shekarar 2025.

Asalin hoton, Twitter/@atiku
"Wadannan masu zuba jari za su samar da ayyukan yi akalla miliyan biyu da rabi a duk shekara sannan su fitar da mutum miliyan 50 daga kangin talauci a cikin shekara biyu," in ji Alhaji Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar dai zai fafata ne da wasu 'yan takarar shugaban kasa da dama ciki har da Shugaba Buhari, wanda ake ganin a tsakanin su ne fafatawar za ta fi zafi.

Asalin hoton, Getty Images
Tarihin Atiku Abubakar a takaice
- Shekararsa 72
- Ya zama gwamnan jihar Adamawa
- Ya yi mataimakin shugaban kasa 1999 zuwa 2007
- Hamshakin dan kasuwa ne
- Ya rike mukami a hukumar Customs
- Ya sha fuskantar zarge-zargen cinhanci da rashawa
- Musulmi ne daga arewacin Najeriya












