Labaran karya: Da gaske 'yan luwadi sun goyi bayan Atiku?

Question mark made out of newspaper
Lokacin karatu: Minti 7

An dora alhakin faruwar rikicin kabilanci da haddasa rudani a tsakanin masu zabe da kuma hawa da saukar darajar kudi kan yada labaran kanzon-kurege.

A yayin da kafar watsa labarai ta BBC ta kaddamar da gagarumin bincike kan labaran bogi a Afirka, mun yi nazari kan labaran kanzon-kurege biyar da suka yi babban tasiri a nahiyar a wata 12 da suka wuce.

BBC
Presentational grey line

1. 'Yan luwadi 'sun goyi bayan Atiku Abubakar'

Mene ne labarin?

Lokacin da Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na dan takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019, wani shafin Twitter na bogi da aka kirkira da sunansa ya wallafa wani sako inda yake yin godiya ga "Kungiyar 'yan luwadi ta Najeriya" bisa goyon bayan da ta yi masa.

BBC
Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

BBC

A sakon, wanda aka ce "Alhaji Atiku Abubakar" ne ya ce matakin farko da zai dauka idan ya zama shugaban kasa shi ne soke dokar da ta haramta auren jinsi daya, wadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sanyawa hannu a 2014.

Dokar ta tanadi hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari, sannan ta haramta auren jinsi daya a Najeriya.

Wane tasiri labarin ya yi?

BBC
Shafin jaridar The Nation

Asalin hoton, The Nation

Bayanan hoto, Yadda wata jaridar Najeriya ta wallafa labarin "'Yan Luwadi sun goyi bayan Atiku"
BBC

Bayan da aka yada labarin a Twitter ranar 14 Oktoba, wasu shafukan da ke watsa labarai a intanet sun wallafa labarin.

Kazalika bayan kwana 12, wasu manyan jaridun kasar, The Nation da Vanguard, suka buga labarin.

Sun rawaito cewa ita ma kungiyar 'yan luwadi mai suna "Diverse" tana goyon bayan Atiku Abubakar domin zama shugaban kasa, tana mai bayyana shi a matsin dan takarar da ke da "sassaucin ra'ayi".

Za a iya amfani da wannan labari na goyon bayan da 'yan luwadi suka yi masa domin yi masa yarfen siyasa.

Malaman addinin Musulunci da na Kirista, wadanda suke adawa da auren jinsi daya, ka iya yin kira ga mabiyansu da kada su zabe shi.

Yaya aka gane labarin kanzon-kurege ne?

Shafin Twitter da aka yi amfani da shi wurin wallafa labarin ba na Atiku Abubakar ba ne. Wannan ne shafinsa na gaskiya, wanda Twitter ta sanyawa alamar shudi.

Kazalika babu wata alama da ke nuna cewa akwai wata kungiyar 'yan luwadi wadda take da suna irin wanda aka fada a cikin sakon na Twitter.

Haka kuma bincike ya nuna cewa babu wani mutum mai suna Spinky Victor Lee wanda aka ce shi ne mai magana da yawun kungiyar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Agence France Press (AFP) ya gano.

BBC
Presentational grey line

2. Shahararren 'yar jarida daga Kenya ya yada yabo na bogi

Mene ne labarin?

Mai gabatar da shirin kasuwanci na tashar CNN, Richard Quest ya ziyarci birnin Nairobi na kasar Kenya a watan Oktoba domin nadar shirinsa na talabijin.

A lokacin ne Julie Gichuru, tsohowar 'yar jarida kuma mai gabatar da labarai ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar 25 ga watan Oktoba cewa Mista Quest na jin dadin ziyar tasa zuwa Kenya.

Ta wallafa wadannan kalaman, tana cewa Mista Quest ne ya fade su.

"Bangaren shakatawa na Kenya ya yi wa sauran bangarori zarra... Ga misali ga ni nan ina cin abincin safe tare da rakuman dawa!

Lallai Bankin Duniya ya yi gaskiya da ya ayyana Kenya a matsayin kasar da masu zuba jari suka fi son zuwa a Afirka. KAI, KENYA TA YI!"

BBC
A false quote shared by former news anchor

Asalin hoton, Twitter

BBC

Wane tasiri labarin ya yi?

Julie na da fiye da mabiya miliyan daya a shafinta na Twitter, tana da mabiya 600,000 kuma a Instagram, saboda haka jim kadan bayan ta wallafa labarin, dubban mutane sun gan shi kuma sun amince da shi.

Mutane da dama sun soke ta domin yadda ta wallafa wannan labarin karyar duk da cewa ta dade tana aikin jarida.

Yaya aka gane labarin na kanzon-kurege ne?

Richard Quest ya ci karo da sakon na Julie a Twitter, kuma bai yi wata-wata ba sai ya karyata labarin. Ga martanin da ya mayar mata.

BBC
Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

BBC

A sakamakon haka Mis Gichuru ta bai wa mabiyanta hakuri a shafinta na Twitter, kuma ta goge wancan sakon na farko da ta wallafa.

BBC
Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

BBC
Presentational grey line

3. An 'binne gawarwakin' 'yan Somaliya a Habasha

Mene ne labarin?

A watan Yuli ne wata tashar talabijin ta tauraron dan Adam mai suna Ethiopian Satellite Television (ESAT) ta nuna wani bidiyo da ke nuna wasu 'yan kabilar Oromo a Habasha na binne gawarwakin 'yan kabilar Somali a wani kabari mara zurfi.

Tashar ta ce an dauki bidiyon ne a yankin Oromo na kasar Habasha, wurin da aka sami kazamin tashin hankali tsakanin kabilun a cikin wannan shekarar.

Wane tasiri labarin ya yi?

BBC
Cameroon video

Asalin hoton, YouTube

Bayanan hoto, Bidiyon ya nuna yadda aka binne wasu gawarwaki a wani kabari wanda ba shi da zurfi
BBC

Tashar BBC Afaan Oromo ta bayyana cewa wannan labarin da kuma yadda aka yada shi a shafukan sada zumunta a Habasha ya janyo mummunan tashin hankali, inda aka kai wa 'yan kabilar Oromo mazauna Djibouti da Somaliya hari.

'Wani dan gudun hijira a makwabciyar kasar Djibouti ya fada wa BBc cewa an yi masu duka, kuma an wawashe shagunansu bayan da aka nuna bidiyon a can.

Yaya aka gane labarin na kanzon-kurege ne?

Bayan mummunan tasirin da wannan bidiyon ya janyo a shafukan sada zumunta, sai wasu suka fara bibiyar sahihancinsa, kuma sai tashar ESAT ta fito fili ta amince cewa bidiyon na bogi ne, kuma "lallai mai iya karkatar da gaskiyar lamari ne" a cikin wani sakon ban hakuri da ta wallafa a kafarta ta YouTube.

An kuma yada wannan bidiyon da babu wanda ya tantance shi a shafukan sada zumunta a watan Yuni game da rikicin yankin renon Ingila da gwamnati a Kamaru, wurin da ke da nisan kilomita 3,000 yamma da Habasha.

Da alama an sauya wasu abubuwa a bidiyon da tashar ESAT TV ta nuna wa masu kallonta, inda aka goya sautin wasu da aka ce wai matasan 'yan Oromo ne suna tayar da hankali a kan sautin bidiyon na ainihi.

BBC
Presentational grey line

4. "Murabus" din Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu

Mene ne labarin?

Ranar 12 ga watan Fabrairu, wani wakilin tashar talabijin ta Afirka ta Kudu mallakin gwamnati, SABC, ya ruwaito cewa shugaba mai ci a lokacin Jacob Zuma ya amince ya yi murabus.

Ya kuma ce yana da "wasu tabbatattun mutane" da Tshepo Ikaneng ya ce sun tabbatar masa da sahihancin rahoton nasa a daidai lokacin da yake bayar da wani rahoto kai tsaye a wajen wani taron jam'iyyar ANC mai mulkin kasar, inda ake tattauna batun shugaban.

Daga nan ne wani dan jaridar kasar ya wallafa rahoton a Twitter.

BBC
Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

BBC

A lokacin kuma Mista Zuma na fuskantar matsi daga sassan kasar na ya sauka daga mukaminsa saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa, kuma jam'iyyarsa ma ta rika kiransa da ya yi murabus.

'Yan kasar kuma na son jin matakin da zai dauka dangane da sauka daga mukami.

Wane tasiri labarin ya yi?

Kudin Afirka ta Kudu, Rand, ya rasa darajarsa bayan da kakakin Mista Zuma ya bayyana babu kanshin gaskiya a cikin rahoton na tashar SABC da ke cewa zai yi murabus ranar 12 ga watan Fabrairu.

BBC
Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

BBC

Yaya aka gane labarin na kanzon-kurege ne?

Kakakin Mista Zuma ya bayyana rahoton a matsayin maras tushe, kuma ya kira shi "labarin kanzon kurege".

Amma bayan kwana uku Mista Zuma ya ajiye aikinsa - a wannan karon babu karya cikin lamarin.

BBC
Presentational grey line

5. Shugaban Tanzaniya 'ya goyi bayan maza su kara aure' don magance karuwanci

BBC
Tanzania President John Magufuli

Asalin hoton, Zambian Observer

BBC

Mene ne labarin?

An wallafa wani labari da ke cewa wai Shugaba John Magufuli na Tanzaniya ya fada wa mazan kasar da su auri mata biyu ko fiye da biyu domin kawo karshen karuwanci a kasar.

Rahoton ya ce shugaban ya fada wa mazan wannan maganar ne a wajen wani "taro da maza kimanin 14,000" suka halarta cewa "kimanin mata miliyan 40 ne idan aka kwatanta da yawan maza su miliyan 30 a kasar da ke da mutane miliyan 70".

Wai kuma wannan karancin mazan ne ya sa ake samun karuwar karuwanci da zina tsakanin mata, kamar yadda shugaban ya ce in ji wannan labarin.

Wane tasiri labarin ya yi?

An fara wallafa labarin ne a jaridar Zambia Observer ta harshen turanci a watan Fabrairun bana, kuma bai ja hankula sosai ba.

Amma sai bayan da aka wallafa shi a harshen Swahili, wanda shi ne harshen 'yan kasar Tanzaniya, a cikin wani shafin intanet mai suna nipasheonline.com ne labarin ya fara jan hankula.

Daga nan ne ya bazu zuwa wani shafin sada zumunta mai farin jini suna Jamii Forums, inda daga nan ya rikide ya zama babban batun da aka yi ta tafka muhawara a kansa, kana ya kuma kara bazuwa zuwa kasashen Kenya da Zambiya da Afirka ta Kudu da ma Ghana.

Yaya aka gane labarin na kanzon-kurege ne?

Kakakin gwamnatin Tanzaniya ya karyata labarin a Tiwita a harshen Swahili, inda ya ce shugaban kasar bai furta wadannan kalaman ba.

Sashin BBC Swahili kuma ya gano wasu dalilan da suka nuna raunin rahoton.

A rahoton na karya, an ce "Mista Magufuli" ya bayyana cewa 'yan Tanzaniya sun kai miliyan 70, inda wai yawan mata yafi yawan maza da miliyan 10.

Amma alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa yawan mutanen Tanzaniya ba su wuce miliyan 60 ba, kuma babu wani bambanci sosai tsakanin yawan maza da na mata.

line
Fake news branding

Wannan labarin na cikin jerin labarai da BBC ke samarwa domin yaki da labaran karya - wanda ya zama wata matsala a fadin duniya dangane da yadda muke yada labarai da yadda muke hulda da duniyarmu.

line