Jami’an tsaron Najeriya 'sun binciki Atiku'

Atiku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Atiku ya isa Najeriya ne daga Dubai inda ya huta sannan ya gudanar da tarukan siyasa
Lokacin karatu: Minti 1

Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP mai hamayya, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jami'an tsaron kasar sun bincike shi ranar Lahadi jim kadan da isarsa Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya koma kasar ne daga birnin Dubai inda ya shafe kwana da kwanaki tare da wasu abokan siyasa da mukarrabansa.

Bai yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka bincike shi ba.

Kawo lokacin wallafa wannan labarin hukumomi ba su ce uffan ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jami'an tsaron sun dauki matakin ne da zummar yi masa barazana.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A cewarsa, "Na iso Abuja da safiyar nan inda jami'an tsaro suka bincike ni da zummar yi min da ma'aikatana barazana."

"Na sha alwashin gina Najeriya yadda babu wani jami'in tsaro da ake biyansa da kudin 'yan kasar domin ya kare su zai rika yi musu barazana," in ji Atiku.

Rahotanni sun ce Alhaji Atiku Abubakar ya je Dubai ne domin hutawa da kuma gudanar da taruka na siyasa gabanin soma yakin neman zabe ranar 13 ga watan Nuwamba.

Wannan layi ne