Atiku da Buhari: Shin matasan Nigeria sun gaza ne?

President Muhammadu Buhari and opposition leader Atiku Abubakar - archive shot, December 2014

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Muhammudu Buhari, (hagu) mai shekara 71 zai fafata da Atiku Abubakar, mai shekara 75

A jerin rahotannin da muke kawo muku daga 'yan jaridar Afirka, a wannan karon babban editan jaridar Daily Trust da ke Najeriya, Mannir Dan Ali ya yi mana nazari kan dalilan da suka sanya kasar da fiye da rabin mazaunanta 'yan kasa da shekara 35 ne, ta tsayar da tsofaffi domin yi mata takara a zaben da za a yi badi.

Ranar da za a gudanar da zabe mai zuwa, dukkan manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya biyu, Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na babbar jam'iyyar hamayya Atiku Abubakar, za su kai shekara 148 a jumlace.

Hakan tamkar wani arashi ne idan aka yi la'akari da guguwar da ta taso lokacin da aka sanya hannu kan dokar da ta rage shekarun tsayawa takara kan mukamai daban-daban a kasar, wadda ake yi wa lakabi "Not Too Young To Run" inda ya zama mai son yin takarar shugabancin kasa zai kasance dan shekara 30 ba 35 kamar yadda yake baya.

Jerin sunayen 'yan takarar shugabancin kasar da hukumar zabe ta fitar ya nuna cewa mutum 76 za su tsaya takarar shugabancin kasa, kuma akwai matasa a cikinsu, wadanda suka hada da dan kasuwa Fela Durotoye, da mamallakin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a shafin intanet, Omowale Sowore da kuma mai sharhi a a jarida Tope Fasua, wadanda ko wannensu shekarunsa 47.

Abin da kowa ya sani dai shi ne, a watan Fabrairu fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin Shugaba Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), wanda zai kai shekara 76 a watan Disamba, da kuma Alhaji Atiku Abubakar, na jam'iyyar the People's Democratic Party (PDP), wanda a watan gobe zai cika shekara 72.

Tsofaffi sun dade da jan ragamar harkokin siyasar kasar don haka tsayawa takarar shugabancin ke da tsada ga duk mutumin da zai tsaya a jam'iyyun da ba wadannan biyun ba ne.

'Hannaye cike da dalar Amurka'

Fiye da rabin mutanen da suka yi rijista domin yin zabe 'yan kasa da shekara 35 ne kuma lokacin da aka soma fafutikar Not Too Young To Run a watan Afrilu an yi fatan hakan zai karfafa gwiwar matasa su shiga a dama da su wurin neman mukaman da za a yi zabe a kansu.

A Nigerian student smiles as she attends independence day celebrations in Lagos in October 1, 2013

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kasar ta kusa cika shekara 20 rabonta da mulkin soja

Hukumar zaben kasar ta ce a tsakiyar watan Nuwamba za a soma yakin neman zabe gadan-gadan.

Yakin neman zaben, kamar wadanda suka gabace shi, zai zama tamkar bukukuwa maimakon ya mayar da hankali kan matsalolin da suka addabi kasar irinsu rashin ayyukan yi ga matasa, ko kuma kudin da ake bukata domin gina tituna da makarantu da sauran abubuwan more rayuwa.

Ganin cewa har yanzu tsofaffi ne suka mamaye harkokin siyasar Najeriya, yanzu tsokanar da ake yi wa matasa ita ce - ko da yake matasa sun samu damar yin takara amma rashin kudi ba zai bar su su yi wani tasiri ba - domin kuwa jita-jitar da aka rika yadawa lokacin zaben fitar da gwani ita ce yadda wasu masu son tsayawa takara suka rika cika hannayen masu kada kuri da dalar Amurka.

'Tsofaffi sun fi hikima'

Shugaba Buhari shi kadai ne mutumin da ya nemi tsayawa takara a jam'iyyar APC.

Sanata Yusuf Datti Baba mai shekara 46 a duniya, wanda ya nemi tsayawa takara a jam'iyyar PDP mai hamayya, ya samu kuri'a biyar kacal daga cikin kuri'u 3,000 da wakilai suka kada.

Manyan 'yan takarar sun zabi mutanen da ba su kai su a shekaru ba domin su kasance mataimakansu.

Shugaba Buhari zai sake tafiya da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, mai shekara 61 a duniya, yayin da Alhaji Atiku Abubakar ya dauki tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi, mai shekara 57 domin ya zama abokin tafiyarsa.

population

Batun gaskiya shi ne manyan jam'iyyun Najeriya biyu sun dade da samun magoya baya, kuma masu ruwa da tsaki kan sha'anin siyasa ba sa son yin kasadar amincewa da matasan da ba su taba gwada shugabanci ba.

Duk da haka, matasan ne suke yin bakin kokarinsu domin kare kasar, su suke aiki tukuru sannan su biya haraji baya ga hankoron da suke yi na inganta iliminsu domin su zama 'yan kasa nagari.

Watakila za su dangana idan suka dauki karin maganar nan da ke cewa "abin da babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai gano ba."

Ko kuma su rika tunanin cewa wasu kasashen duniyar suna da shugabannin da suka tsufa, irin su shugaban Kamaru Paul Biya mai shekara 84, wanda a makon jiya ya lashe zabe karo na bakwai da kuma shugaban Algeria Abdellaziz Bouteflika, mai shekara 81, wanda sau biyar yana tsayawa takarar shugabancin kasar.

Presentational grey line

Ga wasu sharhi da Mannir Dan Ali ya rubuta: