Buhari ya taya Super Eagles murnar zuwa gasar Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun miliyoyan 'yan Najeriya wajen taya 'yan wasan Super Eagles murnar samun gurbin gasar cin kofin Afirka da za a yi a kasar Kamaru a badi.
Super Eagles ta Najeriya ta tsallake ne zuwa gasar bayan ta yi canjaras ci 1-1 da Bafana-Bafana ta Afirka ta kudu a karawar da suka yi a ranar Asabar a birnin Johannesburg.
Sauran kasashen da suka samu gurbin shiga gasar bayan wasannin da aka fafata a jiya sun hada da Uganda da Mali da kuma Morocco.
Najeriya da ta lashe kofin gasar sau uku, wannan ne karon farko da ta samu gurbin shiga gasar bayan kasa tsallakewa sau biyu a baya.
Shugaban Najeriyar ya yi wa 'yan wasan kasar fatan samun nasara a yayin da za su fara shirye-shiryen tunkarar gasar a Kamaru.







