Najeriya ta samu gurbin zuwa gasar Afirka a Kamaru

Wasan ya yi armashi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Najeriya ta samu gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a 2019 bayan 'yan wasan Super Eagles sun yi kunnen-doki da takwarorinsu na Bafana-Bafana da ci 1-1.

An buga wasa ne ranar Asabar a filin wasan FNB da ke Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Najeriya ce ta soma zura kwallo lokacin da dan wasan Afirka ta kudu Buhle Mkhwanazi ya so kade kwallon da takwaransa na Najeriya Samuel Kalu ya buga amma ta fada ragarsu, minti goma da soma wasa.

Afirka ta kudu ta samu damar cin kwallo a minti na 18 bayan dan wasanta Thamsanqa Mkhize ya mika wa takwaransa Lebo Mothiba tamaula amma ya kasa kammala aikin.

A minti na 26 ne Percy Tau ya keta 'yan wasan bayan Najeriya inda ya mika wa takwaransa Mothiba kwallon da bai yi jinkiri ba wajen zura ta aka tashi 1-1.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A sakon da kulob din Super Eagles ya wallafa a Twitter, ya ce "Eagles ta yi tsalle ta koma gasar AFCON."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shugaban majalisar dattawan kasar, a sakon taya murnar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Super Eagles 'kun sanya mu alfahari."