An samu daidaituwa tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu

Shugaban Koriya ta Kudu ya ce Koriya ta Arewa a shirye take ta rufe tashar harba makami mai linzaminta da ke Tongchang-ri a karkashin sa idon kwararru.

A karshen taron kwanaki biyu tsakanin kasashen biyu, Moon Jae-in ya kuma shaida cewa Pyongyang a shirye take ta dau wasu karin matakai, kamar rufe babban cibiyar nukiliyar Yongbyon idan Amurka ta dau matakan da suka dace.

A karon farko, kasashen biyu sun kuma amince da muradai guda na kwance damarar nukiliya a yankunansu, kuma kim jong-un ya alkawarta kai ziyara birnin Seoul nan bada jimawa ba.

Kasashen biyu na kuma fatan gina layin dogo da zai hade kasashen biyu da kuma neman damar daukar nauyin wasanin Olympics na bazara a nan gaba.

Amurka ta bayyana gamsuwarta da tattaunawar tsakanin kasashen biyu, kuma ta ce tana gab da cimma burinta.