Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a yi taron Koriya ta Arewa da ta Kudu
Sama da tawagar jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu, da 'yan jarida da kwararru a bangaren kimiyya da fasaha 90 ne suka tafi makofciyarsu Koria ta Arewa.
Dan fara shirin taron koli mai cike da tarihi, da shugaba Moon Jae-in da Kim Jung-un za su yi a ranar talata mai zuwa.
Wannan shi zai zama karo na 3 da shugabannin kuma makofta za su gana da juna cikin shekarar nan.
Ana sa ran jirgin da zai dauki shugaba Moon zai sauka kai tsaye babban filin jirgin sama da babban birnin Pyongyang.
Ganawar da suka yi ta baya da Kim Jung-un sun yi ta ne a wani kauye mai suna Panmunjom da ke iyakar kasashen biyu.
Kafar yada labaran Koriya ta Arewa ta bayyana taron kolin mai cike da tarihi, inda kasashen biyu da basa gamaci da juna ke kokarin yaukaka dangantakarsu dan kwanciyar hankalin yankin.