Shin halin da Venezuela ke ciki zai iya zama darasi ga kasashe?

Wadannan makudan kudaden da su ake siyan nama kilo daya

Asalin hoton, Reuters

Al'ummar kasar Venezuela na rayuwa a cikin yanayin hauhawar farashi mafi muni da aka taba samu tun bayan yakin duniya na biyu.

Farashin kayayyaki ya kara hauhawa a watan Agusta, inda ya karu da kaso 65,000% a shekara, a cewar Farfesa Steve Hanke, wani masanin tattalin arziki a jami'ar Johns Hopkins da ke Baltimore, kuma daya daga cikin masana kan hauhawar farashin kayayyaki a duniya.

Tun a watan Nuwamban 2016, Venezuela ta shiga cikin kasashen duniya da ke fama da matsanancin hauhawar farashin kayayyaki, inda farashin ke karuwa da kaso 219 a duk wata, sannan kuma ya rubanya a cikin kwanaki 18.

Yanayin da kasar ke ciki ya munana kwarai da gaske, kuma karancin abinci da magungunan da kasar ke fama da su, ya tilastawa 'yan kasar sayen kayan amfanin yau da kullum da tsabar kudi masu yawa.

Farfesa Hanke ya shaida wa BBC cewa, idan aka hada da Venezuela, sau 58 aka taba fuskantar mummunan tashin farashin kayayyaki a duniya, ga misalan irin wannan munanan yanayi guda biyar.

1. Hungary 1946

  • Hauhawar farashi a duk rana: 207%
  • Rubanyar farashi a duk rana: Awa 15
Wannan kudaden kasar Hungary ne

Asalin hoton, Getty Images

A watan Yulin 1946, hauhawar farshin kayayyaki a Hungary ya kai kashi 41.9 cikin 100 a wata, hauhawan da ba a taba gani ba.

Sakamakon hauhawar farashin da ake samu a duk cikin sa'a 15 a kasar, ya sa duk abin da mutum ya ke da shi da safe, to kafin yamma ya kare.

Yakin duniya na biyu Hungary ta yi asarar dukiyarta ko arzikinta da kaso 40 cikin 100, saboda an lalata mata kadarorinta da yawansu ya kai kaso 80 cikin 100, sannan kuma an lalata layin dogo da kuma titunan kasar duk a lokacin yakin duniya na biyun, hakan ya sa ala tilas gwamnatin kasar ta biya diyyar miliyoyin kudin kasar.

Kasar ta sha yunkurin bunkasa darajar kudin kasar, lokacin da 'yan kasar suka fara bambance darajar kudi ta hanyar amfani da launinsu.

A ranar 1 ga watan Agustan 1946, gwamnatin kasar ta kaddamar da wani tsattsauran shiri na daidaita tattalin arzikin kasar wanda ya hada da sauya tsarin haraji da kwato kadarori masu daraja da aka kai kasashen waje da kuma bullo da sabon kudi.

Idan shirin ya fara aiki, Forint daya zai zama daidai da tsohon kudinsu octillion 400.

2. Zimbabwe 2008

  • Hauhawar farashi a kowacce rana: 98%
  • Rubanyar farashi a kowacce rana: A cikin sa'oi 25
An samar da wadannan kudade na kasar Zimbabwe ne bayan kasar ta fuskanci mummunan hahhawar farashin kayayyaki

Sakamakon sauya fasalin shirin mallakar filayen noma mai cike da ce-ce-ku-ce wanda ya hada da kwace gonakin fararen fata a karshen shekarun 1990, Zimbabwe ta fuskanci gagarumin koma baya a bangaren noma.

Wannan yanayi ya tsananta wanda har ya shafi yakin da aka yi a Congo a shekarar 1998, kazalika ya kuma janyo Amurka da kasashen turai suka sanya wa gwamnatin Robert Mugabe takunkumi a 2002.

Bayan shafe shekara 10 da afkuwar wannan lamari, sai farashin kayayyaki suka fara tashin goron zabi.

A watan Nuwamban 2008, hauhawar farashin kayayyaki a kasar sai da ya kai kaso biliyan 79 cikin 100 a wata.

Shaguna kan kara farashin kayayyaki a rana guda sau da dama.

Faduwar tattalin arzkin kasar ya janyo al'ummar kasar shiga halin 'ni 'ya su,' saboda rashin wadataccen ruwan sha da rashin wutar lantarki ga dogayen layuka a bankuna da gidajen mai ga karancin kayayyakin abinci a kasuwanni.

Da yawa daga cikin 'yan kasar sukan tsallaka zuwa kasashen Afirka ta Kudu ko Bostwana domin sayan kayayyaki, hakan ya sa kudaden Amurka wato dala da na Afirka ta Kudu wato rand suka zamo kudaden da ake amfani da su.

3. Yugoslavia 1994

  • Hauhawar farashin kayayyaki a rana: 65%
  • Rubanyar farashi a cikin sa'oi 43
Wannan hotunan mata 'yan kasar Yugoslavia ne da aka dauka a 1992

Asalin hoton, AFP

An kafa kasar Yugoslavia ne bayan yakin duniya na daya wanda hadakar kasashen Bosnia da Herzegovina da Croatia da Macedonia da Montenegro da Serbia da kuma Slovenia suka yi.

Matsalar tattalin arziki da kuma rikicin siyasa a karni na 1980 ne suka janyo ta fada cikin yaki wanda ya haifar da rabewar kasashen zuwa kasashe daban-daban.

A shekarar 1992, kasashen Serbia da Montenegro ne kadai suka zamo a hade.

Asarar da rikicin ya janyo da matsalar tattalin arziki ya sa gwamnatin kasar ta fara buga takardun kudi ba bisa ka'ida ba don cike baitul malinta.

Kashe-kashen kudade ba bisa ka'ida ba da cin hanci da kuma takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanyawa kasar a shekarun 1992 da 1993 ya kara ta'azzara matsalar.

A farkon shekarar 1994, sai farashin kayayyaki ya fara karuwa inda har ya kai kaso miliyan 313 cikin 100 a kowanne wata.

Mutane sun kasance da zarar sun samu kudi sai su yi maza-maza su kashe su.

Wannan matsaloli da ma wasunsu sun sa shugaban kasar na wancan lokaci ya amince ya samar da sabbin kudi.

4. Germany 1923

  • Hauhawar farashin kayayyaki a kowacce rana ya kai kaso 21 cikin 100
  • Rubanyar farashi a rana ya kai kwana uku ko sa'oi 17.
Yara a kasar Jamus na amfani da tsohon kudin kasar suna wasa a 1923

Asalin hoton, Getty Images

Bayan yakin duniya na daya, an bar kasar Jamus da tulin bashi.

Sai da gwamnatin kasar ta fara buga kudi irin na kasar domin sayen kudaden kasashen waje ko ta samu ta biya bashin da ake bin ta.

Yayin da ake buga kudade barkatai ba dadi, sai darajar kudin kasar ta fadi, amma mummunan yanayin da Jamus ta shiga shi ne a shekarar 1923, bayan da ta gaza biyan wasu kudade da ake bin ta.

A watan Octoban 1923, farashin kayayyaki ya fara hawa inda har ya kai kaso dubu 29, 500 cikin 100, inda aka rinka samun hauhawar farashin kayayyaki a duk cikin kwanaki uku zuwa hudu.

Biredin da ake sayansa a kan kudin kasar 250 a farko shekara, sai da ya kai miliyan dubu 200 a watan Nuwambar shekarar.

Wannan dalili ya sa ala tilas gwamnatin kasar ta bullo da sabbin kudi, hakan ya taimaka mata al'amura suka dai-daita.

5. Greece 1944

  • Hauhawar farashin kayayyaki a kowacce rana ya kai kaso 18%
  • Ana samun rubanyar farashin kayayyaki a cikin kwana hudu da sa'oi shida
Nan wani ginin tarihi ne a kasar Girka

Tattalin arzikin Girka ya sha fama a lokacin da kasashen duniya suka mamaye ta a yakin duniya na biyu.

Kasashen da suka mamaye ta sun kwashe mata albarkatun kasa da dabbobi da kuma abinci.

Wanna dalili ya sa kasar ta samu koma baya ta fuskar amfanin gona, hakan kuma ya sa aka samu bala'in karancin abinci a manyan biranen kasar, a takaice dai kasar ta fuskanci matsananciyar yunwa.

Yawan harajin da kasar ke karba ya taimaka wajen hauhawar farashin kayayyaki inda ya kai koluluwa zuwa kaso dubu 13 da 800 cikin 100 a watan Nuwambar 1994.

Koda yake tashin farashin kayyakin bai yi kamari kamar na kasashen Hungary da Jamus ba bayan yakin duniyar.

Yunkurin da Girka ta yi wajen daidaita al'amura a kasar ya dauki lokaci fiye da saura kasashen.