Kun san yadda za ku tsira daga hadarin jirgin sama?

Photo of wreckage and rescue workers at the scene of crash in Mexico

Asalin hoton, EPA/Handout

Bayanan hoto, Rahotanni sun ce jirgin da ya fadi a jihar Durango na Mexico ya rasa injunansa biyu

Labarin da ke cewa dukkanin fasinjoji 103 sun tsira a wani hadarin jirgin saman da aka samu a jihar Durango na Mexico ranar Talata ka iya kama da wani abin al'ajabi, musamman idan aka yi la'akari da hotunan baraguzan jirgin da ke (konewa da) hayaki.

Kusan dukkanin wadanda suke cikin jirgin sun ji ciwo, sai dai kuma yawancinsu sun bar wurin da hadarin ya auku ne da ciwo.

Wane irin abin alajabi ne wannan? Abun mamaki, aukuwarsa ba zai yi wuyar da za ka yi tunani ba.

Wace irin dama muke da ita na tsira daga hadari?

A takaice, babu wata amsa kai tsaye - kamar yadda ba za mu iya bayyana yadda za a iya tsira daga hadarin mota ba, domin ya dogara ne bisa yanayin aukuwar hadarin.

Amma a lokacin da Hukumar Kiyaye Haddura a Harkar Sufuri ta Amurka, ta gano cewar sama da kashi 95 cikin 100 na mutane sun tsira daga hadduran, ciki har da kashi 55 cikin 100 na hadduran da suka fi muni.

Damarmakinmu sun dogara ne kan wasu dalilai kamar kamawa da wuta da nisan wurin da aka yi hadarin a sama da kuma wurin da aka yi hadarin.

A cikin wani bincike da Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayyar Turai ta gudanar a shekarar 1996, an gano cewar a na iya kare aukuwar kashi 90 cikin 100 na hadduran jirgin sama.

Submerged US Airways plane pictured in Hudson River

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 2009, fasinjoji 150 sun tsira daga wani jirgin da bya lume a kogin Hudson na birnin New York'

Tafiya ta hanyar jiragen sama ta fi sauki kan tafiye-tafiye kan sauran hanyoyin sufuri kuma ta fi rashin hadari idan aka kwatanta da adadin hadduran da ake samu a sauran hanyoyin sufurin, amma wannan ba ya hana wasunmu fargaba.

Ta yiwu hakan ta faru ne domin muna yawan ganin haddura masu muni ne a cikin labarai ko kuma ta wasan kwaikwayon masana'antar fina-finan Hollywood.

Mene ne yake sa a gane in za a iya tsira daga hatsari?

Tom Farrier, tsohon darakta ne na kiyaye haddura a kungiyar kamfanonin jiragen sama na kasuwa (Air Transport Association), ya yi bayani a kan shafin Quora cewar wasu sharruda uku ne suke taimaka:

  • Ko abubuwan da mutanen dake cikin jirgi suka ci karo da su na cikin abubuwan da mutum zai iya jurewa
  • Idan jirgin da suka shiga bai lalace sosai ba
  • Idan yanayin wurin da suka fada bayan hadarin jirgin ya yi barazana nan take ga mutanen ko kuma masu ceto

A takaice: wane irin aibi ko wane bugu ya yi wa jiki da kuma mene ne matakin ta'adin da ya yi wa jirgin da kuma irin hatsarin da ke tattare da baraguzan jirgin da kuma wurin da abin ya faru.

A hadarin da aka yi a Mexico, jirgin ya fadi ne jim kadan bayan ya tashi kuma yawancin fasinjojin jirgin sun samu sun tsere kafin jirgin ya kama da wuta.

A man with an amputated leg is pictured resting during rehab class

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Nuwambar 2016, mutum 71 sun mutu a cikin wani jirgin da ya dauko 'yan wasan wata kungiyar kwallon kafa a Brazil, Chapecoense. Mutum shida ne kawai suka tsira - ciki har da Jakson Follmann (da yake cikin wannan hoton)

Da aka tambaye shi kan ko faduwa a kasa ko kuma akan ruwa ne ya fi muni, masani a kan sufurin jiragen sama Adrian Gjertsen ya ce tsira ya fi danganta ne kan kusancin masu aikin ceto fiye da kan wurin da jirgi ya fada.

Ya shaida wa BBC cewar: "Alal misali, a lokacin da aka samu hadari a kan kogin Hudson, an samu masu aikin ceto nan take. Amma idan kana tsakiyar teku, za a samu karin matsala ta samun kai wa ga kan tudu."

"Idan aka samu hadari a Sahara ko kuma a tsakiyar tekun Atlantic - ba zan iya cewa akwai bambanci tsakaninsu ba, tunda dai babu wanda zai taimaka a wurin"

Ta yaya za mu kara damarmakinmu?

Intanet na cike da shawarwari kan wannan maudu'in: saka damarar kujerar da kin saka riga mai saurin kamawa da wuta da kuma kirga layin kujeru tun daga farko saboda yiwuwar mutuwar hasken wutar lantarki.

Mutane suna muhawara kan inda ya fi rashin hadari mutum ya zauna a cikin jirgi, kuma wasu bincike sun nuna cewar zama a baya ka iya kasancewa mafi karancin hadari.

Mr Gjertsen ya ce ba abu ne mai sauki ba. Ya danganta da irin jirgin da kuma irin hadarin.

Bayanan bidiyo, Air Steward: "No one pays attention to the in-flight demonstration".

Ya ce "Daya daga cikin lamuran da ke janyo matsaloli shi ne yadda matafiya ke son tsira tare da kayansu".

"Wannan na iya shafar tsaron lafiya, ba ma tasu ba kadai, har da ta kowa".