Kalli hotunan zanga-zangar da Kiristoci suka yi a Jos

zanga-zangar jos
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar suna neman gwamnati ta dauki mataki game da hare-haren da aka kai kauyukan jihar

Daruruwan Kiristoci sun yi zanga-zanga a birnin Jos na jihar Filato ,domin nuna rashin jin dadinsu game da kashe-kashen da aka yi a wadansu kauyukan jihar.

Masu zanga-zanga da suka sanya bakaken tufafi sun bazu a titunan birnin dauke da kwalayen wadanda aka rubuta sakonni iri daban-daban.

Shugabannin al'umma a yankin da lamarin ya faru sun ce rikicin ya yi sanadiyyar "mutuwar mutum fiye da 200, amma 'yan sanda a jihar sun ce mutum 86 ne aka kashe."

Wadansu kwalayen na dauke da sakonnin da ke kira ga Shugaban Amurka Donald Trump da ya kawo musu dauki.

A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai Yakubu Dogara game da batun, kwana guda bayan ya kai ziyara jihar.

Masu zanga-zangar sun fito
Bayanan hoto, 'Yan sanda sun ce mutum 86 aka kashe a rikicin
Kiristoci masu zanga-zanga
Bayanan hoto, Shugabannin al'umma a jihar sun ce wadanda aka kashe sun "haura mutum 200"
Kiristoci masu zanga-zanga
Bayanan hoto, An yi imanin cewa kashe-kashen sun biyo bayan wani harin da aka kai wa wasu makiyaya Fulani
Kiristoci masu zanga-zanga
Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya ziyarci jihar a ranar Talata, inda ya nemi jama'a su kai zuciya nesa.
Kiristoci masu zanga-zanga
Bayanan hoto, Sai dai masu zanga-zangar suna ganin matakan da gwamnati ke daukawa sun yi kadan