Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda rikicin Filato ya shafa
Wadansu daga cikin wadanda suka jikkata a hare-haren da aka kai wasu kauyuka 11 na jihar Filato suna asibiti inda ake ba su kulawa.
Wani shugaban al'umma a jihar ya shaida wa BBC cewa akalla mutum 200 aka kashe, amma 'yan sanda sun ce 86 ne suka rasa rayukansu.
Sannan wasu da dama ba a san adadinsu ba sun samu raunuka.














