Mahaukaciyar guguwa ta hallaka mutum 100 a Indiya

Asalin hoton, PTI
Akalla mutum 95 ne suka hallaka yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da mahaukaciyar guguwa mai dauke da kasa ta afkawa jihohin Uttar Pradesh da Rajasthan a arewacin Indiya.
Guguwar ta lalata turakun wutar lantarki da bishiyoyi da gidaje da kuma dabbobi a ranar Laraba.
Da dama daga cikin wadanda suka rasa rayukansu na barci ne lokacin da gidajensu suka rufta bayan da tsawa mai karfin gaske ta afkawa gidajen.
Mahaucikaciyar guguwar mai dauke da kasa, aba ce da aka saba gani a wasu sassan Indiya a lokacin zafi amma ba a taba samun asarar rayuka irin wannan ba .
Mutum 64 suka hallaka a jihar Uttar Pradesh, 43 daga cikinsu a lardin Agra inda a nan ne fittacen ginin nan na Taj Mahal yake.
Jami'ai sun ce watakila adadin ya karu.
Bishiyoyi da bangon da suka fado sun kashe mutane da dama a jihar.
Gwamnan jihar Yogi Adityanath ya umurci jami'ai a kan su tabbatar sun sa ido kan aikin rarraba kayan jin kai.
Kwamishinan aikin jin kai na jihar Sanjay Kumar ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Indiya PTI cewa gwamnatin jihar "ta nemi a samar mata da cikakken rahoto dangane da abinda ya faru a wuraren da matsalar ta fi kamari".

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, AFP
Mahaukaciyar guguwar ta kuma shafi wasu yankuna da suka hada da Rajasthan da Alwar da Bharatpur da Dholpur inda mutum 31 suka hallaka.
Jami'ai sun ce guguwar ta yi barna sosai a yankin Alwar .
An dai rufe makarantun da ke yankin.

Gwamnatin jihar ta kuma yi shelar biyan diyyar rupee 400,000 kwatankwacin dala 4,400 ga iyalan mamatan.

Asalin hoton, AFP











