Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: 'Yan majalisar kasa nawa ne suka mutu kwanan nan?
- Marubuci, Raliya Zubairu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
Rasuwar Senata Mustapha Bukar ita ce ta baya-bayanan a cikin jerin 'yan majalisun dokoki da suka rasu a Najeriya. A baya dai ba kasafai manyan 'yan siyasar ke rasuwa ajere-ajere ba kamar haka, abin da ya sa lamarin ke ci gaba da daukar hankalin jama'a a kasar.
Sanatan mai wakiltar mazabar Daura a jihar Katsina ya rasu ne da safiyar ranar Laraba ,kamar yadda iyalinsa suka bayyana.
Shugaba Muhammadu Buhari, wanda suka fito daga mazaba daya da sanatan, ya ce ya kadu da mutuwarsa yana mai cewa "babban rashi ne" ga al'ummar kasar.
Zuwa yanzu babu wani bayani da aka samu kan musabbabin rasuwar dan majalisa, wanda ya rasu yana da shekara 64.
Marigayin wanda injiniya ne, an haife shi ne a garin Daura a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1954.
Mun yi waiwaye kan wasu daga cikin 'yan majalisar da suka rasu a baya-bayan nan:
Sanata Ali Wakili
A ranar 17 ga watan Maris Sanata Ali Wakil da ke wakiltar mazabar Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya ya rasu.
Marigayin ya rasu yana da shekara 58 a duniya.
Babu wani bayani da aka samu dai kan musabbabin rasuwar marigayin, sai dai an yi ta yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa kwana daya kafin ya rasu ya halarci daurin auren diyar Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka, da aka yi a Kano.
Wane ne Sanata Ali Wakili?
- An haife shi a shekarar 1960, ya mutu yana da shekara 58
- Dan asalin karamar hukumar Tafawa Balewa ne a jihar Bauchi
- Ya kammala digirinsa a Jami'ar Bayero da ke Kano a 1982
- Ya dade yana aiki a Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya tun daga 1984
- Ya zama sanata mai wakiltar Bauchi Ta Kudu a 2015
- Shi ne shugaban kwamitin Yaki da Talauci na majalisar dattawa
- Ya rasu ranar 17 ga watan Maris na 2018
- Ya bar mata biyu da 'ya'ya 10.
Bayanai: Daga Majalisar Dattawa da iyalinsa
Hon Umar Buba
Hon Umar Buba Jibril da ke wakiltar mazabar Lokoja da ke jihar Kogi a majlisar wakilan Najeriya ya rasu a karshen watan Maris yana da shekara 58 a duniya.
Kafin ya rasu shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan ta kasa.
Ya kuma taba zama kakakin majalisar dokoki ta jihar Kogi.
Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya bayyana shi a matsayin mutumin da ba ya kunbiya-kunbiya, mai kishin kasa, wanda kuma yake da kwarewar shugabanci.
Dogara ya kara da cewa Hon Jibril yana aiki tukuru kuma ya cancanci wakiltar jama'arsa.
Shugaban majalisar ya kuma yi alhini kan yadda abokan aikinsa da dama suka rigamu gidan gaskiya a baya-bayan nan.
Sai dai ya ce haka mahalicci ya tsara kuma kowanne dan'adam zai bar duniya.
Hon Independence Ogunewe
A ranar Talata ne tsohon dan Majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Ahiazu da Ezinihitte a jihar Imo a Maalisar wakilai ta kasa shi ma ya rasu.
Ya mutu yana da shekara 57 a duniya.
Rahotanni sun ce ya mutu ne a gidansa da ke Abuja kuma kawo yanzu babu masaniya kan musabbabin mutuwar tasa.
Ya wakilci jama'ar mazabarsa daga shekara ta 2003 zuwa 2011.
An haife Hon Ogunewe a birnin Warri a ranar 22 ga watan Afrilu na 1960.
Hon Bello Sani
Hon Bello Sani da ke wakiltar mazabar Mashi da Dutsi a jihar Katsina a majlisar wakilan Nijeriya ya rasu a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Ya rasu yana da shekara 51 da haihuwa a duniya.
Ya taba zama shugaban Karamar Hukumar Mashi a jihar ta Katsina.
Sannan an ta ba zamarsa wakili a majalisar dokoki ta jihar Katsina.
A lokacin da ya rasu, Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ya bayyana shi a matsayin mutum mai faran-faran da jama'a kuma mai aiki tukuru.