'Yan majalisa sun girmama marigayi Sanata Ali Wakili

'Yan majalisar wakilai da na dattawan Najeriya sun yi wani zama na musamman don girmama marigayi Sanata Ali Wakili.

Sanata Ali Wakili, wanda ke wakiltar Bauchi Ta Kudu a majalisar dattawan kasar, ya rasu ne a ranar Asabar a Abuja babban birnin kasar.

Babu wani bayani da aka samu dai kan musabbabin rasuwar marigayin, sai dai an yi ta yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa ko a ranar Juma'a ma ya halarci daurin auren diyar Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka, da aka yi a Kano.

Tun a ranar Asabar din aka yi jana'izar Sanata Wakili a babban masallacin kasa da ke Abuja kamar yadda musulunci ya tanada, inda daga bisani aka koma garin Bauchi don ci gaba da zaman makoki.

A zaman na ranar Talata, 'yan majalisar sun yi addu'o'i na musamman ga marigayin, tare da bayyana irin kyawawan halayensa da ayyukan ci gaban da ya yi wa kasar.

Kakakin majalisar Yakubu Dogara ya bayyana rashin Sanata Wakili a matsayin wani abu da ya shafi kasa baki daya, ba al'ummar Bauchi Ta Kudu kawai ba.

Kalaman Dogara kan marigayin

"Hakika rashin Sanata Wakili abu ne da zai shafi iyalansa da 'yan uwansa da abokansa da masu kaunarsa a kafafen sada zumunta da al'ummar mazabarsa da kuma takwarorinsa na majalisa.

Kuma rashin nasa zai taba mutane sosai a karamar hukumar Tafawa Balewa da jihar Bauchi da Najeriya da ma duniya baki daya.

Mutum ne mara kumbiya-kumbiya, mai kokarin kwatowa talaka hakkinsa da girmama dimokradiyya.

Mutum ne mai yawan kare muradun al'ummarsa a majalisar dattawa.

Ya yi fafutika wajen ganin an samu shugabanci na gari musamman a jiharmu ta Bauchi da Najeriya baki daya.

Sanata Waliki bai taba kasa a gwiwa ba don kawo ci gaba duk da irin yadda wasu masu mummunar akida ke masa barazana".

Wane ne Sanata Ali Wakili?

  • An haife shi a shekarar 1960, ya mutu yana da shekara 58
  • Dan asalin karamar hukumar Tafawa Balewa ne a jihar Bauchi
  • Ya kammala digirinsa a Jami'ar Bayero da ke Kano a 1982
  • Ya dade yana aiki a Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya tun daga 1984
  • Ya zama sanata mai wakiltar Bauchi Ta Kudu a 2015
  • Shi ne shugaban kwamitin Yaki da Talauci na majalisar dattawa
  • Ya rasu ranar 17 ga watan Maris na 2018
  • Ya bar mata biyu da 'ya'ya 10.

Bayanai: Daga Majalisar Dattawa da iyalinsa

A karshe 'yan majalisar sun mika sakon ta'aziyyarsu ga iyalansa da al'ummar mazabarsa da masarautar Bauchi da majalisar dattawa da al'ummar Bauchi da na Najeriya baki daya.

Karin labaran da za ku so ku karanta: