Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: Yadda aka kama 'shahararren mai safarar makamai'
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta sanar da cewa ta kama wani mutum da take zargi da safarar bindigogi a kasar, wanda ke cikin jerin sunayen mutanen da take nema ruwa a jallo.
Ana zargin Jonah Abbey, wanda aka fi sani da Jonah IDI, da sayar da makamai ga kungiyoyin masu tayar da kayar baya a jihohi da dama na kasar.
A wata sanarwa da hukumar DSS ta aike wa manema labarai a ranar Lahadi, ta ce tawagoginta sun yi aiki tukuru cikin kwana 10 da suka gabata inda suka kama masu aikata manyan laifuka da dama.
Kawo yanzu mutanen da ake zargin ba su ce komai ba game da sanarwar jami'an tsaron, kuma ba a bayyana lokacin da za a gurfanar da su a gaban kotu ba.
Sanarwar ta ce an yi nasarar kama masu satar mutane don karbar kudin fansa da masu safarar bindigogi da masu satar shanu wadanda ke ayyukansu a jihohin Filato da Taraba da Benue.
Najeriya na fama da rikice-rikice da suka shafi addini da kabilanci, inda ake amfani da muggan makamai ba tare da sanin inda jama'a ke samunsu ba.
Jami'an tsaro sun ce an shafe shekara 10 ana neman Abbey, ruwa a jallo.
A cewar sanarwar: "A ranar 13 ga watan Maris ne da misalin 12.20 na rana aka yi nasarar kama Mista Abbey a garin Wukari na jihar Taraba tare da direbansa Agyo Saviour wanda aka fi kira da Dan-Wase.
"Wasu bayanan sirri na baya-bayan nan sun nuna cewa Mista Abbey ya aiki direbansa Saviour da makamai da harsasai daga Konduga a jihar Borno zuwa jihar Taraba."
'Shigo da makamai ya karu'
Hukumar DSS ta ce Mista Abbey yana da abokan kasuwanci a jihohin Filato da Ebonyi da Cross River da Enugu da Bayelsa.
"Kuma alamu sun nuna cewa yana samun makaman ne daga Jamhuriyyar Kamaru da kuma wasu sassan Arewa Maso Gabashin Najeriya," in ji DSS.
Hukumar ta kuma ce ta kama wani mai satar mutane don kudin fansa Lawal Ibrahim da aka fi sani da Alhaji Awalu a Angwan Rogo da ke kan titin Bauchi a birnin Jos.
"Shi ne wanda ake zargi da kashe wani ma'aikacin gwamnatin jihar Filato Daanan Balgnan, a ranar 30 ga watan Disambar bara, kuma yana da hannu a wasu sace-sacen mutane a jihohin Nasarawa da Kaduna da Bauchi," in ji DSS.
Kazalika kuma a ranar 7 ga watan Maris ne jami'an DSS suka kama wani babban kwamandan "gungun 'yan ta'adda" na Terwase Akwaza da aka fi sani da Ghana, wato Sesugh Aondoseer, a kusa da babbar kasuwar Makurdi ta jihar Benue.
Ana zarginsa da kitsa sace mutane da dama da fashi a Katsina Ala-Ukum da Gboko-Makurdi da kuma Takum a jihar Taraba.
An samu kudi kimanin naira miliyan 1.5 a hannunsa, wanda wani bangare ne na kudin fansa da suka karba bayan sace iyalan jami'in wata hukumar gwamnati.
Ba ya ga rikicin addini da na kabilanci, da satar mutane don kudin fansa, akwai kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda shi ma ke kara bazuwa a fadin kasar.
Hakan dai ya jawo asarar dumbin rayuka a kasar da kuma dukiyoyi, duk kuwa da kokarin da gwamnati ke cewa tana yi don kawo karshen wadannan matsaloli.
A makon da ya gabata ne wani rahoto na masana'antar kera makamai ta duniya wanda Cibiyar Binciken zaman lafiya ta Stockholm ta fitar, ya ce an samu karin shigar da makamai da kashi 42 cikin 100 a Najeriya cikin shekara hudu da suka gabata.
A shekarar 2017 ma hukumar fasa kwauri ta kwastom ta sha kama daruruwan binbdigogi da aka shigo da su kasar ba bisa ka'ida ba ta jihar Lagos, inda ake zargin daga Turkiyya aka shigo da su.
Sai dai ba a sake jin komai kan batun ba tun bayan da Shugaba Buhari ya ziyarci kasar Turkiyya a watan Oktobar 2017.