Kenya: Kenyatta da Odinga sun gana a karon farko

Shugaban Kenya da madugun adawa sun yi alkawalin cewa za su fara tattaunawar sulhu bayan zaben da aka gudanar a bara wanda ya nemi jefa kasar cikin rikici

Uhuru Kenyatta da babban mai adawa da shi Raila Odinga sun gana a Nairobi babban birnin kasar a yau Juma'a.

Wannan ne karon farko da mutanen biyu masu hamayya da juna suka gana tun bayan zaben da aka gudanar a bara mai cike da kalubale.

Ganawarsu na zuwa ne sa'o'i kafin sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fara ziyara a kasar.

Uhuru Kenyatta da Raila Odinga a karon farko sun yi jawabi a kafar talabijin din kasar.

Kimanin mutane 150 aka kashe bayan bayyana sakamakon zaben.

A watan Janairu ne Mista Odinga ya rantsar da kansa a matsayin "shugaban al'ummar Kenya" bayan ya ki amincewa da sakamakon zaben da aka bayyana Mista Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasara.

A baya dai dukkaninsu sun yi watsi da tayin tattaunawa.

Amma a yayin ganawar da suka yi a yau Juma'a, shugaba Kenyatta ya kira Mista Odinga a matsayin dan uwa.

Kuma Mista Kenyatta ya ce: "Za mu fara tattauna batutuwan da suka haifar da sabani a tsakaninmu"

"Za mu amince da duk wani goyon baya daga kowane shugaba da kuma al'ummar Kenya domin gina sabuwar kasa tare da tabbatar da hadin kai."

A nasa bangaren, Odinga ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen sabani.

Kenyatta ne dai ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Oktoba, da kashi 98 na yawan kuri'u.

Odinga kuma ya fice ne a zaben zagaye na biyu, kafin daga baya ya rantsar da kansa a matsayin shugaban al'umma.