Kullum ranar soyayya ce a addinin Musulunci – Sheikh Daurawa

Asalin hoton, Getty Images
Bahaushe mutum ne mai tsananin rikon al`adunsa, kuma galibin Hausawa Musulmi ne, wadanda kunya da koyarwar addinin ke taka muhimmiyar rawa a harkokinsa na rayuwa.
A ranar Laraba ne ake bikin ranar masoya ta duniya; shin yaya Hausawa ke kallon wannan rana?
'Yan magana dai kan ce soyayya kogi ne, kuma idan ba ka sha to ka ratsa.
Don haka kamar sauran bil`adama, Hausawa masoya kan nuna zunzurutun kauna ga junansu, amma saboda al`adar kunya ba kasafai suke nuna soyayyar a fili ba.
Hatta a ranar masoya irin ta yau, kuma birni irin Kano mai miliyoyin Hausawa, a ziyarar da na kai wuraren da jama`a kan taru, wadanda na gani suna magagin soyayya kalilan ne.
Ganin yadda Hausawa ke dogaro ga addini wajen kaurace wa ranar Valantine, wakilin BBC a Kano Ibrahim Isa tuntubi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, babban Malamin addinin Musulunci kan ko da wani lokaci da Musulmi kan yi bikin soyayya?
- Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da shi:







