Ko kun san asalin bikin hawan sallar gani?

Bikin hawan sallar gani na daya daga cikin bukukuwan da masu sarauta da kuma dawaki ke kece raini a cikinsa.
A kan yi wa dawakai ado irin na alfarma da burgewa.
Masu gudanar da wannan biki dai sun ce biki ne mai tarihin gaske da ake yi tun zamanin Bayajidda wanda ke hada kan sarakunan kasar hausa a lokacin, amma bayan zuwan addinin musulunci sai aka yi masa kwaskwarima.
Masarautar Daura na daga cikin wadanda ke gudanar da wannan biki, kuma wakilin BBC Ibrahim Isa ya halarci bikin na bana inda ya samu tattauna wa da Alhaji Usman Yaro, sarkin labaran masarautar Daura wanda ya masa karin bayani a kan bikin.
Alhaji Usman Yaro ya ce " sallar gani ta samo asali ne tun lokacin zuwan Bayajidda kasar Hausa, kalmar gani ta samo asali ne saboda duk lokacin da sarki ya shigo zai je ya sanar da mai martaba cewa gani na iso.Kuma an kirkireta ne domin gyara tafiyar da sha'anin mulki."
A wajen wannan biki dai sarki kan tattauna da hakimansa a kan muhimman batutuwan da suka shafi talakawansu.

Ba al'ummar Daura ce kadai ke gudanar da wannan biki na hawan sallar gani ba, Masarautar Gumel da Hadeja a jihar Jigawan Najeriya kan yi bikin hawan sallar ganin, saboda su ma sun gada ne tun kaka da kakanni.
Mutane da dama dai kan halarci wannan biki na hawan sallar gani domin kashe kwarkwatar idanunsu.












