Hotunan yadda aka yi bikin sallah a kasashen duniya

Kasashe daban-daban sun soma bikin karamar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan. Ga hotunan yadda aka yi bikin sallah a wasu kasashe.

A group of girls is greeted by a woman during the Muslim holiday of Eid al-Fitr, in the village of Dalgamon, Tanta, some 120km north of Cairo, Egypt, 25 June

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masar da wasu kasashen Larabawa sun soma bikin karamar Sallah ranar Lahadi, bayan an bayyana ganin sabon wata a hukumance. Wadannan wasu mata ne da ke shagulan sallah a kauyen Dalgamon da ke kilomita 120 daga arewacin Alkahira.
Iraqi girl celebrates Eid al-Fitr in Mosul, 25 June

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan yarinyar 'yar kasar Iraqi ta yi kwalliya a birnin Mosul da yaki ya daidaita, inda mazaunansa suka yi sallah a karon farko cikin shekaru da dama sakamakon hare-haren mayakan IS.
Muslim worshippers leave the Blue Mosque after the Eid al-Fitr prayers in Istanbul, 25 June

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Musulmi a birnin Istanbul na Turkiyya sun yi sallar su ne a masallacin nan na Blue Mosque da ke da dimbin tarihi
Syrian President Bashar al-Assad (2nd L) attends prayers in Hama, 25 June

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad (na biyu daga hagu), wanda ke ci gaba da zama a kan mulki bayan am kwashe shekara shida ana yakin basasa, ya yi sallah ne a birnin Hama.
Muslims pray on the street in Moscow, 25 June

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Musulmi a Moscow, babban birnin Rasha sun yi sallah ne a kan titin da ke kusa da babban masallacin birnin - ba a ginawa Musulmi masallacin idi, wadanda akasarinsu 'yan ci-rani ne daga Tsakiyar Asia.
Kyrgyz Muslims pray in central Bishkek, with a monument of Soviet State founder Vladimir Lenin seen in the background, 25 June

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A kasar Kyrgyzstan, Musulmi sun yi sallah ne a kan titi.
Palestinian Muslims attend the Eid al-Fitr prayer in an open area of Gaza City, 25 June

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wadannan matan Palasdinawa ne da suka yi sallah a birnin Gaza. A wannan makon ne Masar ta soma bai wa ma'aikatar wutar lantarkin Palasdinu mai domin sanya wa a injinan wutarta, abin da ya saukaka yadda ake biyan kudin wuta.
Muslim women walk after praying during Eid al-Fitr at a mosque inside the city hall compound in Marawi City, Philippines, 25 June

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojojin Philippine sun yi shelar tsagaita bude wuta a babban birnin da Musulmi suka fi rinjaye Marawi, inda suke yaki da kungiyoyin Musulmi masu tayar da kayar baya.
Members of Southwark's Muslim community pose for a photograph during Eid celebrations in Dulwich Park, London, 25 June

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wadannan mazauna birnin London suka dauki hoto a wurin shakatawa na Dulwich.