Saad Hariri: Farayi Minsitan Lebanon ya dakatar da murabus

Firai Ministan Lebanon Saad Hariri, ya "dakatar da" murabus din da ya bayar da sanarwar cewa ya yi a Saudiyya makonni biyu da suka wuce, wanda ya haifar da ce-ce ku-ce.

Mista Hariri ya ce shugaban kasa, Michel Aoun, ya roke shi ya dakatar da murabus din gabanin tattaunawar da za a yi.

Sun tattauna ne kwana daya bayan Mr Hariri ya koma Lebanon.

Mista Hariri ya musanta cewa Saudiyya ce ta tilasta masa yin murabus kuma ta tsare shi, a kokarin dakile tasirin Iran da kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran din a Lebanon.

"Na gabatar da murabus dina ga shugaban kasa, kuma ya roke ni in dan dakata," in ji Mr Hariri bayan taron da aka gudanar Laraba a fadar shugaban kasa a Baabda.

Mista Hariri ya ce Lebanon tana bukatar sadaukarwa ta musamman a wannan lokaci domin kare ta daga fuskantar matsaloli da kalubale.

Za a iya kallon jinkirta murabus din Saad Hariri a matsayin wani koma-baya ga Saudiyya.

Mutane da dama sun yi imanin Saudiyya ce ta tilasta masa yayin murabus din domin rusa gwamnatin Lebanon.

Mista Hariri ya bar Riyadh zuwa Faransa a karshen mako tare da matarsa ​​da daya daga cikin 'ya'yansa uku.

Ya tafi Lebanon a ranar Talata, ya kuma yada zango a Masar da Cyprus.

Mista Hariri ya yi murabus daga mukaminsa a wani jawabin da ya gabatar a gidan talbijin a ranar 4 ga watan Nuwamba daga birinin Riyad na Saudiyya, inda ya zargi Iran da kitsa rikice-rikce a yankin, sannan ya yi zargin cewa ana yunkurin hallaka shi.