Saad Hariri: Farayi Minsitan Lebanon ya dakatar da murabus

Supporters of Saad Hariri wave Future Movement flags as they celebrate in Beirut on 21 November 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Mr Hariri sun yi ta murnar komawarsa Lebanon a ranar Talata da daddare

Firai Ministan Lebanon Saad Hariri, ya "dakatar da" murabus din da ya bayar da sanarwar cewa ya yi a Saudiyya makonni biyu da suka wuce, wanda ya haifar da ce-ce ku-ce.

Mista Hariri ya ce shugaban kasa, Michel Aoun, ya roke shi ya dakatar da murabus din gabanin tattaunawar da za a yi.

Sun tattauna ne kwana daya bayan Mr Hariri ya koma Lebanon.

Mista Hariri ya musanta cewa Saudiyya ce ta tilasta masa yin murabus kuma ta tsare shi, a kokarin dakile tasirin Iran da kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran din a Lebanon.

"Na gabatar da murabus dina ga shugaban kasa, kuma ya roke ni in dan dakata," in ji Mr Hariri bayan taron da aka gudanar Laraba a fadar shugaban kasa a Baabda.

Mista Hariri ya ce Lebanon tana bukatar sadaukarwa ta musamman a wannan lokaci domin kare ta daga fuskantar matsaloli da kalubale.

Za a iya kallon jinkirta murabus din Saad Hariri a matsayin wani koma-baya ga Saudiyya.

Mutane da dama sun yi imanin Saudiyya ce ta tilasta masa yayin murabus din domin rusa gwamnatin Lebanon.

Mista Hariri ya bar Riyadh zuwa Faransa a karshen mako tare da matarsa ​​da daya daga cikin 'ya'yansa uku.

Ya tafi Lebanon a ranar Talata, ya kuma yada zango a Masar da Cyprus.

Mista Hariri ya yi murabus daga mukaminsa a wani jawabin da ya gabatar a gidan talbijin a ranar 4 ga watan Nuwamba daga birinin Riyad na Saudiyya, inda ya zargi Iran da kitsa rikice-rikce a yankin, sannan ya yi zargin cewa ana yunkurin hallaka shi.

A handout picture shows Lebanese President Michel Aoun (L) and Prime Minister Saad Hariri (R) meeting at the presidential palace in Baabda, outside Beirut (22 November 2017)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Michel Aoun ya sadu da Saad Hariri a fadar shugaban kasa kwana guda bayan komawar firai ministan kasar ta Labanon