Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ashura: An ta da bam a masallacin 'yan Shia
Wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa da kuma mutum biyar a wani masallacin 'yan Shia a birnin Kabaul na kasar Afghanistan, yayin da ake shirye-shiryen ranar Ashura.
Maharin ya boye kansa ne a matsayin makiyayi don samun damar isa masallacin, kamar yadda wani jami'in dan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Maharin ya isa wurin ne da garken dabbobinsa gabanin ya tayar da bam din da ke jikinsa," kamar yadda wani ganau ya ce.
Kungiyar da ke ikirarin kafa Daular Musulunci (IS) ce ta dauki nauyin kai harin.
Akalla mutum 20 ne suka jikkata sanadiyyar harin.
Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce adadin mutanen da harin ya shafa zai iya karuwa.
Ana zaton cewa an hari masallacin 'yan Shi'a na unguwar Qala-e Fatullah a birnin Kabul ne, amma sai bam din ya tashi gab da masallacin.
A bara ma kimanin mutum 14 suka mutu a hubbaren Karte Sakhi yayin shirye-shiryen ranar Ashura.
Galibin Musulmin Afghanistan mabiya Sunni ne, amma akwai mabiya Shi'a kimanin kaso 10 zuwa 20 cikin 100 na jama'ar kasar.