Damisa ta bayyana a dajin Yankari bayan gomman shekaru

Wannan shi ne hoton damisar da kamara ta dauka

Asalin hoton, WSC Nigera

Bayanan hoto, Wannan shi ne hoton damisar da kamara ta dauka

An bayar da rahoton ganin damisa a dajin Yankari da ke jihar Bauchi a arewacin Najeriya, inda a baya ake zaton karewar irin wadannan manyan namun dawa masu kama da kyanwa.

A da an san Gandun dajin na Yankari da zakuna, da giwaye, amma dai wannan ne karon farko da aka ga damisar cikin shekaru gommai.

Hukumar gandun dajin Yankari ta wallafa hotunan damisar a shafinta na Facebook, inda take nuna jin dadinta dangane da wannan lamari.

Hukumar ta Yankari ta ce an ga hoton damisar ne a wata kamarar bidiyo ta kungiyar da ke kula da bai wa namun daji kariya, wacce ita ce ta dauki hoton damisar.

Gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ina farin cikin ganin yawan dabbobi daban-daban na karuwa a Gandun Dajin Yankari.

"Akwai riba a bai wa namun daji kariya. Muna fatan dabbobi da yawa su dawo dajin Yankari," in ji gwamna Abubakar.