Damisa ta bayyana a dajin Yankari bayan gomman shekaru

An bayar da rahoton ganin damisa a dajin Yankari da ke jihar Bauchi a arewacin Najeriya, inda a baya ake zaton karewar irin wadannan manyan namun dawa masu kama da kyanwa.

A da an san Gandun dajin na Yankari da zakuna, da giwaye, amma dai wannan ne karon farko da aka ga damisar cikin shekaru gommai.

Hukumar gandun dajin Yankari ta wallafa hotunan damisar a shafinta na Facebook, inda take nuna jin dadinta dangane da wannan lamari.

Hukumar ta Yankari ta ce an ga hoton damisar ne a wata kamarar bidiyo ta kungiyar da ke kula da bai wa namun daji kariya, wacce ita ce ta dauki hoton damisar.

Gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ina farin cikin ganin yawan dabbobi daban-daban na karuwa a Gandun Dajin Yankari.

"Akwai riba a bai wa namun daji kariya. Muna fatan dabbobi da yawa su dawo dajin Yankari," in ji gwamna Abubakar.