'Jawabin Buhari ya yi hannun riga da halin da ake ciki a Nigeria'

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ne a ranar Talata

Jawabin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata, yana ci gaba da jan hankalin wasu 'yan kasar musamman a shafukan sada zumunta.

Yayin da wasu ke ganin cewa shugaban bai yi daidai ba, wasu gani suke ya yi abin da ya kamata.

Osasu Igbinedion gani take ya kamata Shugaba Buhari ya warkar da kansa kafin ya nemi bai wa makwabtansa magani.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, 'yar Najeriyar ta ce: "Jawabin Buhari a zauren Majalisar Dinkin Duniya wani lamari ne na cire datti a idon makwabci, gabanin mutum ya cire daga nasa idon."

Osasu

Asalin hoton, TWitter

Bayanan hoto, Akalla mutum 406 ne suka yayata sakon da Osasu Igbinedion ta wallafa a shafinta na Twitter

Shima Onye Nkuzi ya ce jawabin shugaban Najeriyar ya yi hannun riga da abin da yake faruwa a kasarsa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce jawabin shugaban bai zo da mamaki ba, yana mai karkare sakon da tambayan kan cewar "kwana nawa shugaban ya yi a Najeriya cikin wannan shekarar?"

Onye Nkuzi

Asalin hoton, TWitter

Bayanan hoto, Mutum 76 ne suka yayata sakon Onye Nkuzi

Sai dai kuma, Ezeaka Chidozie ya mayar da hankali kan zargin adadin motocin da Shugaba Buhari ya tafi da su birnin New York, idan aka kwatana da na tsohon Shugaban Kasar Goodluck Jonathan a lokacinsa.

Ya ce yayin da Buhari ya je da motoci hudu, motocin da tsohon "Shugaba Jonathan ya isa wurin ne da motoci 30."

hjhjaj

Asalin hoton, TWitter

Linus Hagher ya ce "duka nahiyar Afirka tana tare da Shugaba Buhari yayin da yake gabatar da jawabi a gaban zauren majalisar. Amma wadansu 'yan Najeriya suna nuna rashin jin dadinsu game da jawabin."

hjaja

Asalin hoton, Facebook