Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi a sauya fasalin Majalisar Dinkin Duniya ta yadda za ko wace bangare duniya za ta samu wuri a kwamitin tsaro na majalisar.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta dauki mataki kan musgunawar da ake yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

A jawabin da ya gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72, Shugaba Buhari, ya ce irin abun da yake faruwa a Myanmar ya yi kama da irin kisan kiyashin da ya aka yi Bosniya a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994.

Mutane a sassan duniya sun yi ta Allah-wadai kan irin musgunawa da ake yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar.

Shugaba Buhari ya kuma yi tsokaci kan matsalar Falasdinawa, inda ya nemi Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka musu wajen samar da kasa inda za su ci gashin kansu.

Ya ce a dukkan rikice-rikicen da ke faruwa, mata da yara ne suka fi fadawa cikin matsala.

Da yake tsokaci kan kasarsa Najeriya kuma, Shugaba Buhari ya ce kasar za ta ci gaba da goyon bayan MDD a duk wani kokarinta, wanda suka hada har da shirin samar da ci gaba mai dorewa a duniya nan da shekarar 2030.

"Tun lokacin da kasar ta shiga majalisar a shekarar 1960, Najeriya take ba da gudumawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya," in ji Shugaba Buhari.