Shiga BBC Hausa a wayar salula

Za a iya samun wani bangare na shafin yanar sadarwa na BBC Hausa a kan wayar salula, da karamar komfuta ta hannu, ko kuma sauran na’urori na wayar iska da ake rikewa a hannu.
Jeka gurbin yanar sadarwa a wayar salularka sannan ka rubuta:
<link type="page"><caption> http://www.bbchausa.com/mobile</caption><url href="http://www.bbchausa.com/mobile" platform="highweb"/></link>
Zaka iya adana wannan shafi a bangaren shafukan da kake sha’awa, ta yadda za a same shi duk sanda ake bukata.
Idan ba ka da tabbas ko zaka iya samun damar shiga yanar sadarwa a wayar salular ka, tuntubi wadanda suka samar maka da layi.
Farashi
Gwargwadon irin yarjejeniyar da kake da ita, za a iya cazar ka wasu kudade saboda samun damar shiga shafukan yanar sadarwa ta wayar salula.
Idan baka da tabbas kan yawan kudaden da za a caje ka dan yin amfani da yanar sadarwa a wayar salularka, tuntubi wadanda suka samar maka da layin waya.
Zai iya yiwuwa an kara wasu ‘yan kudade kan cajin da ake yi maka a cikin kudaden da kake biya.
Haka kuma zaka iya zabar ‘dunkullallen tsari’ ko ‘pakitin shafukan yanar sadarwa’ wanda za a iya biya duk wata domin samun caji mai sauki wajen shiga yanar sadarwa.
Amma BBC ba ta cajin kudi domin a sami bayanai ta wayar salula.










