Sarakunan da suka nuna turjiya ga Turawan mulkin-mallaka a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 7
Fiye da shekara 100 tun bayan da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye Najeriya, har yanzu tarihi bai manta irin abubuwan da suka faru a lokacin ba.
Turawan mulkin mallakar sun fara zuwa Najeriya ne tare da mamaye Legas a shekarar 1861.
Turawan sun fafata da al'umomin da suka samu duka gauruwan da suka shiga.
A wasu garuruwan Turawan sun samu nasarar karɓe ikonsu daga hannun sarakunansu ba tare da wata Turjiya ba.
To amma a wasu garuruwan Turawan sun fuskanci turjiya daga sarakuna da ke jagorantarsu a garuruwan kafin su samu nasarar ƙwace su.
Dalilai uku da suka kawo Turawa Najeriya
Dakta Abdullahi, malami a sashen nazarin tarihi na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce Turawa sun shigo ƙasar da a yanzu ake kira Najeriya ta hanyoyi guda uku da suka haɗa da:
Yawon buɗe idanu: Masanin tarihin ya ce hanya ta farko da Turawa suka zo Najeriya ita ce hanyar yawo buɗe idanu.
Dokta Abdullahi ya ce su ake kira 'explorers', wato sun zo ƙasashen Afirka domin nazarin yadda ake rayuwa a ƙasashen da irin ma'adinan da ke yankunan.
Yaɗa addini: Masanin tarihin ya ce hanya ta biyu da turawa suka shigo Najeriyaita ta hanyar haɗa addinin Kirista.
Ya ƙara da cewa su ne ake kira da ƴan mishan, wato masu yaɗa addinin kiristanci.
Mulkin mallaka: Dokta Abdullahi ya ce hanya ta ƙarshe da turawa suka shigo Najeriya ita ce don yi wa ƙasar mulkin mallaka.
''A lokacin ne kuma ya fuskanci turjiya daban-daban a wasu yankunan Najeriya'', in ji masanin tarihin.
A cikin wannan muƙala mun duba wasu daga cikin sarakunan da suka nuna turjiya ga Turawan mulkin mallakar.
Sarkin Musulmi Attahiru

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Musulmi Attahiru na daga cikin mutanen da suka nuna bijirewarsu kai-tsaye ga Turawan mulkin mallaka.
Sarki Muhammadu Attahiru, shi ne Sultan na ƙarshe kuma na 12 a jerin Sarakunan Musulunci tun daga mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodio, kafin Turawan mulkin mallaka su ƙwace iko da Daular.
Lokacin mulkinsa na cike da gwagwarmaya ta zuwan Turawan mulkin mallaka waɗanda suka fara shiga arewacin Najeriya a shekarun 1890.
Dakta Abdullahi ya ce Sultan Attahiru ya jagoranci mayaƙansa suka bijire wa Turawan, lamarin da ya kai ga yaƙi har Turawan suka fitar da shi daga ƙasarsa, kafin daga baya su kashe shi a wani gari da ke cikin jihar Gombe ta yanzu.
Muhammadu Attahiru II
Shi ma Muhammadu Attaihu wanda ya zo daga baya, bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen bijire wa Turawan, kamar yadda Dakta Abdullahi ya bayyana.
Muhammadu Attahiru, ya yi mulki ne daga 1903 -1915.
Turawa ''Sun naɗa shi ne da nufin samun iko da Daular, to amma sai ya ƙi bayar da kai bori ya hau, saboda yana sane da abin da ya faru da mahaifinsa'', in ji masanin tarihin.
Bayan haka nuna alamun ba zai bi umarninsu ba, shi ma daga baya sun yaƙe shi.
Sarkin Kano Alu (Babba)

Asalin hoton, Hussaini Idris
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Abdullahi ya ce Sarki Alu da ya mulki Kano daga 1894 -1903 ya kasance cikin fitattun sarakunan arewacin Najeriya da suka bijirewarsu ga turawan mulkin mallaka.
Alu ko Aliyu Babba ko kuma Alu Maisango shi ne wanda ya zamo Sarkin Kano daga lokacin yaƙin basasa a 1895 zuwa lokacin da Turawan mulki mallaka suka ƙwace mulki daga hannunsa a 1903.
Kuma a kan hanyar Sarki Alu ta komawa Kano ne daga Sokoto suka samu labarin cewa Turawa sun shiga Kano abin da ya sa suka yada zango a Kwatarkwashi domin tattauna abin yi nagaba.
"Shi Sarki Alu ya kama hanya zuwa Gabas kuma jama'arsa suka bi shi domin guje wa Turawa to amma ƙaddara ta riga fata, inda ya haɗu da Turawa a kan hanyarsa ta zuwa Makka kuma sun kama shi suka tafi da shi inda suka kai shi Adamawa."
A nan ya zauna ya samu kamar shekara biyu kafin su mayar da shi zuwa Lokoja inda a nan ya rayu da iyalinsa har zuwa 1926 lokacin da ya rasu." in ji Dr Raliya Zubair Mahmour, masaniyar tarihi kuma malama a tsangayar tarihi da ke kwalejin Kumbotso College a Kano.
Shehun Borno, Mai Bukar Garbai
Shehun Borno, Mai Bukar Garbai na daga cikin sarakunan arewacin Najeriya da suka nuna wa turawan mulkin mallaka jarumta.
''Shi a lokacinsa ya yi yaƙi da Turawan manyan ƙasashen turai biyu, wato na Birtaniya da na Jamus'', in masanin tarihin.
Ya gwabza da Turawan Jamus da na Birtaniya.
Turawan Jamus sun shiga Daular Borno daga arewacinta, sannan da Turawan Birtaniya da suka shiga daga yammaci, kamar yadda ya bayyana.
''Sai dai daga ƙarshe shi ma an kashe shi a shekarar 1890'', a cewar Dakta Abdullahi.
Sarkin Bida - Etsu Nupe - Abubakar

Asalin hoton, Masarautar Bida
Etsu Nupe wato Sarkin Nupe ko kuma Sarkin Bida - Etsu Abubakar, wanda ya yi sarauta a shekarar 1897 zuwa 1901, shi ma ya kasance daga cikin sarakunan gargajiya na arewacin Najeriya da suka nuna tirjiya ga Turawan mulkin mallaka, kamar yadda Dakta Abdullahi ya yi bayani.
Wannan masarauta ta Etsu Nupe wato babban sarkin gargajiya na al'umma ko kabilar Nufawa tana garin Bida ne da ke jihar Naija.
Oba Ovonramwen Nogbaisi
Oba Ovonramwen Nogbaisi, wanda kuma ake kira Overami, ya kasance daya daga cikin fitattun sarakunan gargajiya daga yankin kudu maso yammacin Najeriya wato yankin kabilar Yarabawa da suka nuna turjiya da Turawan mulkin-mallaka.
Oba Ovonramwen wanda ya kasance babban sarkin Masarautar Benin ya yi mulkin wannan babbar masarauta daga 1888 zuwa 1897. Kuma ya kasance Sarkin masarautar na 35.
Sarkin ya ja da Turawan mulkin-mallaka kan tsarin kasuwancinsu da bai yarda da shi ba da kuma mulkinsu, inda ta kai har ya yi yaki da su, in ji masanin tarihi, Dakta Abdullahi.
Alake na Egba
Akwai sarakuna na ɓangaren Abeokuta waɗanda ake kira Egba Chiefs ko Alake Councils, waɗanda suka yi mulki a ƙarshen ƙarni na 19 su ma sun nuna turjiya ga Turawanb mulkin-mallaka, kamar yadda Dakta Abdullahi ya ce.
Ya ce, Turawan sun so su ƙaƙaba musu mulkin-mallaka wanda ba su samu nasara ba har sai 1nda suka yanko wani yankin suka saka shi ƙarƙashin mulkin mallakar Najeriya, bayan an haɗe kudu da arewa a 1914.
Akwai fitattun zanga-zanga ko tarzoma ko turjiya da aka yi a yankin na ƙabilar Yarabawa ga Turawan mulkin mallaka, kuma ɗaya daga cikin fitattu da aka yi shi ne Iseyin-Okeiho na 1916.
Turjiyar yankin ƙabilar Igbo
Fitacciyar tarzoma da ke da alaƙa da bijire wa Turawan mulkin-mallaka a yankin kudu maso gabashi na Najeriya wato yankin ƙabilar Igbo, ita ce tarzomar da mata 'yan kasuwa suka yi a Aba, a 1929 wadda ake kira ''Aba Women Riot'', in ji masanin.
Tarzomar kuwa ta biyo bayan tsarin haraji da Turawan suka ɓullo da shi ne da matan waɗanda ke harkokin kasuwanci za su rinƙa biya, abin da suka ƙi yarda da da shi.
Sarakunan Igbo - Arochukwu
Haka kuma an samu turjiya da ta haddasa tarzoma da faɗa a kan mulkin Turawan, tsakanin sarakunan al'ummar Arochukwu, na yankin ƙabilar ta Igbo, daga shekara ta 1901 zuwa 1902.
An yi wannan tashin hankali ne kuwa a sanadiyyar dokoki na kasuwanci da tsarin haraji da Truwan mulkin-mallaka suka nemi sanya wa al'ummar a wannan lokaci, bayan shekara da shekaru da aka yi ta tattaunawa abu ya ci tura.
Sannan an samu ire-iren wannan tarzoma da turjiya kan mulki da tsare-tsaren Turawan, a yankin Nsukka da kewaye na ƙabilar ta Igbo a tsakanin shekarun 1910 zuwa 1920.
Turjiyar Al'ummomin Tsakiyar Najeriya
Sarakuna da al'ummomi da ke yankunan da a yau ake kira Tsakiyar Najeriya wadanda suka unshi jihohi irin su Benue da Nasarawa da Filato da Abuja da wasu sassan jihar Kaduna, an samu abilu da su ma suka nuna turjiya da bore a kan tsare-tsaren da Turawa suka kawo a lokacin.
Daga cikin ire-iren waɗannan akwai waɗanda aka yi a bauchi da kuma waɗanda sarakunan ƙabilar Tivi da ke yankin jihar Benue suka yi a tsakanin shekarar 1010 zuwa 1930.
Al'ummomin da sarakunansu sun nuna turjiya ga Turawan a kan neman kawo tsarin mulki na gama-gari, wanda hakan ya janyo tarzoma.
Haka su ma sarakuna da al'ummomin yankin kamar jihar Filato a yau sun bijire wa yunkurin Turawan na mullkin-mallaka na kawo musu sauye-sauye a harkar mulki da kuma kasuwanci
Wace irin turjiya sarakunan suka nuna?
Waɗannan sarakuna sun bijire wa Turawan ne ta hanyoyi daban-daban, kamar huɗu da suka haɗa da:
1- Turjiya da makami
2- Turjiya ta Aƙida
3- Turjiya ta tsarin mulki
4- Turjiya ta tattalin arziƙi
Dakta Abdullahi ya yi bayanin cewa, sarakuna da al'ummomin sun bujire wa Turawan mulkin-mallakar ta waɗannan hanyoyi da muka jero a sama.
Sarakunan gargajiya sun yi amfani da makamai na gargajiya irin su kwari da baka da adduna da masu da takobi yayin da su kuma Turawa suka yi amfani da bindigogi na zamani a yaƙe-yaƙen da aka yi a wancan lokaci na bijirewar.
Dangane da aƙida kuwa Sarakuna musamman na yankin da a yau yake na arewacin Najeriya sarakunan lokacin kamar sarkin Musulmi Attahiru da sarki Alu na Kano sun yaƙi Turawan ne musamman saboda addini, kasancewar tuni al'umma tana da tsarin addini da take bi na Musulunci da kuma al'adu, a don haka suka nuna turjiya ga duk wani abu da Turawan suka zo musu da shi da ya saba wannan aƙida da al'ummarsu take a kai.
Akwai kuma magana ta tsarin mulki wadda ita ma ta wannan fanni sarakuna da al'ummomin da Turawan suka nemi mulka a lokacin sun turje musu sakamakon zuwa da irin tsare-tsarensu na tafikarwa da Turawan suka zo da shi wanda ya saɓa tsarin da sarakunan suke a kai. A don haka wannan ya zama wani dalili na nuna turjiya ga Turawan.
Haka kuma tsarin tattalin arziki musamman harkar kasuwanci da haraji wannan ma ya kasance wani abu da sarakunan da al'ummominsu suna nuna turjiya a kai kasancewar suna da hanyoyi da tsarinsu na al'ada da suke gudanar da kasuwancinsu, saɓanin da Turawan da suka nemi tilasta musu karɓa su jingine nasu na gargajiya.
Tsarin haraji da Turawan suka zo da shi ya kasance babban abin da ya janyo turjiya daga al'umma da sarakunan lokacin, da kuma neman a yi watsi da tsarin gargajiya na cinikayya na ban-gishiri-in-ba-ka-manda.
Sannan akwai tsarin ɗibar mutane musamman maza masu mayawa kuma majiya ƙarfi da turawan suka zo da shi - inda mutanen za su riƙa yin ayyuka misali na hanya ko titin jirgin ƙasa - wanda wannan ya zama kamar wani aiki ne na gwale-gwale. wannan ma ya kasance wani dalili da al'umma suka nuna turjiya ga Turawan na mulkin-mallaka.










