Iƙirarin aikata kisan ƙare dangi a Gaza ya janyo suka ga 'yar majalisar Amurka

Asalin hoton, Getty Images
'Yan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican a Amurka sun ɓullo da wasu matakai guda biyu na hukunta wata 'yar jam'iyyar Dimokrat, a daidai lokacin da dukkan jam'iyyun ke sukar kalaman da ta yi game da yaƙin Isra'ila da Gaza.
Rashida Tlaib, wadda ta kasance Ba'amurkiya ƴar asalin Falasɗinu ɗaya tilo a majalisar dokokin Amurka, ta wallafa wani bidiyo, tana zargin Shugaba Joe Biden da goyon bayan kisan ƙare dangi a Gaza.
Fadar White House da 'yan jam'iyyar Dimokrat da dama sun soki lamirin bidiyon da ma sauran kalaman 'yar majalisar.
Misis Tlaib ta ce abokan aikinta sun "fi mayar da hankali kan yadda za su rufe min baki maimakon ceton rayuka".
A wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ranar Juma'a, Rashida Tlaib ta aika jawabinta kai tsaye ga Shugaba Biden tare da yin kira a tsagaita wuta.
Bidiyon yana kuma ɗauke da jawabin Mista Biden da ke bayyana goyon bayansa ga Isra'ila, sai kuma na waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata a Gaza da kuma zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a faɗin Amurka.
"Joe Biden ya goyi bayan kisan ƙare dangi da ake yi wa al'ummar Falasɗinu," kamar yadda ƙarshen bidiyon ya bayyana. "Mutanen Amurka ba za su manta ba."
Bidiyon ya kuma nuna yadda mutane ke rera taken "daga bakin kogi zuwa teku", wanda ke kira ga Falasɗinawa su ƙwace iko da dukkan filayen da ke tsakanin Kogin Jordan har zuwa tekun Bahar Rum, ciki har da Isra'ila.
Ƙungiyoyin Yahudawa kamar Anti-Defamation League sun ce taken kira ne na rusa ƙasar Isra'ila.
Hakan dai ya ci karo da ra'ayin wasu masu fafutukar goyon bayan Falasɗinawa waɗanda suka ce galibin mutanen da ke rera taken suna kira ne a kawo ƙarshen mamayen da Isra'ila ke yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma ƙofar ragon da ta yi wa Gaza, ba wai rusa Isra'ila kanta ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rashida Tlaib da ke wakiltar gundumar Michigan da ta haɗa da wasu sassan Detroit da Dearborn, tana ɗaya daga cikin Musulmai guda uku a Majalisar dokokin Amurka.
Ta daɗe tana harzuƙa shugabannin jam'iyyar Dimokrat da ƙungiyoyin da ke goyon bayan Isra'ila saboda irin sukar da take yi wa Isra'ila.
Da take kare kalaman nata, Rashida ta ce taken "kira ne na neman 'yanci da tabbatar da 'yancin ɗan'adam, da zaman tare cikin kwanciyar hankali da lumana, ba mace-mace da ɓarna, ko ƙiyayya ba".
Sai dai kalaman sun jawo suka daga lungu da saƙo, ciki har da abokan ƙawancen jam'iyyar Dimokrat na jiharta.
A wani saƙon Tuwita ga 'yar majalisar, Babbar Lauyar Michigan, Dana Nessel ta kira kalaman Rashida Tlaib da "masu tayar da hankali".
Misis Nessel ta rubuta cewa "Na goyi bayanku kuma na kare ku sau da yawa, ko da lokacin da kuka faɗi abin da ba za a iya karewa ba, saboda na yarda cewa ku mutane ne na gari. Don Allah ki janye wannan muguwar magana da kuma ƙiyayya," kamar yadda Ms Nessel ta rubuta.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban majalisar dattawan Michigan Jeremy Moss, ɗan jam’iyyar Dimokrat, ya ce kalaman Misis Tlaib kan Yahudawa sun yi muni.
A ranar litinin, attajiri ɗan jam'iyyar Republican a jihar Georgia McCormick ya gabatar da wani kuduri na yin Alla-wadai da Ms Tlaib saboda "ta kira a ruguza ƙasar Isra'ila da kuma yaɗa labaran karya".
A halin da ake ciki, sauran 'yan Democrat a Majalisa, kamar Pramila Jayapal daga Washington, ta ki yin watsi da kalaman Ms Tlaib.
Jon Finer, mataimakin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na fadar White House, ya faɗa a ranar Lahadin da ta gabata cewa gwamnatin Biden ta ki amincewa da "Maganganun ƴar majalisar da kuma kalamai da aka yi amfani da su wajen kwatanta wannan rikici".
Ƴan Isra'ila sama1 da ,400 aka kashe a hare-haren Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.
Tun daga wannan lokacin, sama da Falasɗinawa 10,000 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza.
Zuwa yanzu dai gwamnatin Biden ta daina yin kira da a tsagaita wuta, amma ta ƙara yin taka tsantsan a kalamai da take yi kan rikicin yayin da take ƙoƙarin daidaita muradun da ke karo da juna.
Mista Biden dai ya sha nanata cewa yana goyon bayan ‘yancin da Isra’ila ke da shi na kare kanta, yayin da yake ƙoƙarin ganin an dakatar da yaƙin da ake yi, don ba da damar kai kayan agaji, abinci da kuma ruwa a Gaza.











