'Jirgi mai saukar ungulu na shugaban Iran ya yi muguwar sauka'

Asalin hoton, IRAN PRESIDENTIAL WEBSITE
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce wani jirgi mai saukar ungulu da ke cikin tawagar shugaban Iran ya yi hatsari.
Kawo yanzu ba a sani ba ko shugaban na Iran, Ebrahim Raisi na cikin jirgin, wanda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ce ya fuskancin matsalar.
Ministan cikin gida na ƙasar ya ce masu aikin ceto na ƙoƙarin isa wurin da lamarin ya faru sakamakon mummunan yanayin da ake fuskanta a wajen.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce shugaban ƙasar Ebrahim Raisi na kan hanyarsa ta zuwa birnin Tabriz, da ke arewa maso yammacin ƙasar, bayan dawowarsa daga kan iyakar ƙasar da Azerbaijan, inda ƙaddamar da aikin buɗe wata madatsar ruwa.
Daga cikin mutanen da ke cikin tawagar shugaban akwai ministan harkokin ƙasashen waje, Hossein Amirabdollahian, da gwamnan lardin Azerbaijan ta gabas, Malik Rahmati, da limamin Juma'a na Tabriz, Muhammad Ali Al Hashem.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar IRNA, ya ce "mummunan yanayi da gajimare na kawo tarnaƙi ga ayyukan ceto.
Lamarin ya faru ne kilomita 50 daga arawacin birnin Tabriz.
Dan majalisar dokokin ƙasar mai wakiltar birnin, Ahmad Alirezabeigi, ya shaida wa manema labarai a birnin Tehran cewa har yanzu masu aikin ceto ba su iya gano inda jirgin da ke ɗauke da shugaban ƙasar yake ba.
To sai dai ya ce cewa wasu jiragen biyu da ke cikin tawagar sun sauka lafiya.
Gidan talbijin na ƙasar ya nuna yadda al'ummar ƙasar ke gudanar da addu'o'in samun lafiya ga shugaban ƙasar a birnin Mashhad.
Rashin kyawun yanayi - na ruwan sama da gajimare, na kawo cikas kan aikin ceton a wurin da lamarin ya faru mai tsaunuka.
Kawo yanzu ba a san halin da mutanen da ke cikin jirgin suke ba.
Wane ne Ebrahim Raisi?
An kallonsa a matsayin wanda zai iya gadon jagoran addinin ƙasar Ayatollah Khamenei, a matsayinsana mai tsattsauran ra'ayin siyasa.
Raisi, mai shekara 63, ya zama mataimakin mai shigar da ƙara a Tehran a lokacin yana da shekara 25.
Raisi ya bai wa masu hasashe mamaki a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2017, inda ya zo na biyu a zaɓen.
A shekarar 2019, jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Khamenei ya bayyana sunansa a matsayin wanda zai jagoranci ɓangaren shari'ar ƙasar.
A watan Yunin 2021 ne aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar.










