Ƴan Jam’iyyar APC kawai zan mara wa baya a zaben 2023 - Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa mambobin Jam'iyyarsa ta APC kaɗai zai mara wa baya a babban zaɓen ƙasar na 2023.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce ba zai goyi bayan tsofaffin ƴan APC ko ma ƴan siyasar da suka gurfanar da APC a gaban kotu ba.
Sanarwar da aka fitar ranar Laraba ta ce "Buhari ya kasance soja mai ladabtarwa na APC kuma a zaɓen da ke tafe, zai mara baya ne kawai ga ƴan takarar Jam'iyyar."
"Wannan gargaɗi ne ga ƴan jam'iyyar da suka sauya sheƙa da wadanda suka kai sahihan ƴan takarar APC kotu, su sani cewa ba ma tare da su kuma kar wani daga wajen Jam'iyyar da ya alaƙanta kansa da Shugaba Buhari.
"Shugaba Buhari yana son a ambato shi yana cewa shi ne yake riƙe da kujerar shugaban ƙasa da yardar Allah wanda ya yi amfani da Jam'iyyar APC wajen ba shi karagar mulki da kyakykyawan sakamako a 2015."
A cewarsa, a 2019 ma ya lashe mafi yawan ƙuri'un da aka kaɗa kuma a karon farko da wani wanda ba ɗan PDP ba ya ɗare kan mulki bayan shekara 16 tana mulki.
Abin da Shugaban ƙasar ke cewa a kullum shi ne "ba zan yi yaudara ba ko kuma cin dunduniyar jam'iyyata ta hanyar marawa wasu ƴan takarar da ba na APC ba baya," in ji sanarwar.
A sanarwar, Shugaba Buhari ya jaddada cewa furucinsa ko ɗaya ba wai yana sukar wani ɗan takara ba ne, sai dai ya ce maganar da ya yi ta nuna ƙarara cewa ƴan takarar da APC ta tsayar ne kawai za su samu goyon bayansa kuma sune waɗanda zai yi wa yaƙin zaɓe.
"Muna maraba da duk wani goyon baya daga sauran jam'iyyu ga ƴan takararmu a matakai daban-daban."
Shugaban ya kuma ce zai ci gaba da goyon bayan jam'iyyar a matakai daban-daban domin tabbatar da ɗa'a da daidaito da kuma yin aiki tare.
Ya kuma umarci jami'an da ke ciki da wajen Fadar Shugaban ƙasa da waɗanda suke tattaunawa su guji furta kalaman da za su janyo ce-ce-ku-ce da za su cutar da jam'iyyar da gwamnati ta yadda za a samar da makamin da ƴan hamayya za su yi amfani da shi wajen sukar gwamnati da APC ko ƴan takararta a zaɓe mai zuwa.











