Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya rantse da Al-Kur’ani ba zai yi tazarce ba

Buhari

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi rantsuwa da girman Kur'ani cewa ba zai zarce a mulki karo na uku ba.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar ranar Juma'a.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ya yi a Makkah da wasu zaɓaɓɓun 'ƴan Najeriya mazauna garin.

"Na ranste da Al-Kur'ani mai tsarki zan yi aiki da abinn da kundin tsarin mulki ya tanada kuma zan tafi a lokacin da wa'adina ya ƙare," in ji Buhari.

"Ba na so wani ya fara magana ko yin kamfe a kan tsawaita abin da ba ya cikin kundin tsarin mulki. Ba zan lamunci haka ba."

Kazalika, Shugaba Buhari ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin inganta amfani da fasaha wajen gabatar da zaɓukan ƙasar.

"Samar da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a da rijistar masu zaɓe ta intanet addu'o'ina ne da Allah Ya amsa na cutarsa da aka yi sau uku a wasu zaɓuka a baya," a cewar sanarwar.

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa: "Bayan faɗuwar da na yi a karo na uku, sai na ce, 'Allah Yana nan.' Abokan hamayyata sun yi min dariya amma Allah Ya amsa addu'o'ina ta hanyar kawo fasaha. A wannan gaɓar, babu wanda zai iya sace ƙuri'a ko saya."

Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar tasa a Saudiyya da yin Sallar Juma'a a Masallacin Ka'aba, inda ya ce zai ci gaba da bin kundin tsarin mulki sau da ƙafa a duk ayyukansa kuma zai dinga sa ido da bibiyar ayyukan ministocinsa kamar haka.

Ya ba da tabbaci a wajen taron cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen inganta rayuwar 'yan Najeriya a cikin sauran lokacin da ya rage masa na wata 18, "zan yi hakan ne saboda ƙasar," ya ce.

Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa 'yan Najeriya mazauna Saudiyya kan wakiltar ƙasar yadda ya kamata wajen gyara ƙimarta a idon duniya.

Buhari

Asalin hoton, Haramain Sharifain

'A dinga yi min adalci'

Sannan ya yi magana kan masu sukarsa a Najeriya inda ya ce su dinga yi wa mulkinsa adalci a koyaushe, yana mai cewa su duba yanayin tsaro a yankunan arewa maso gabas da kudu maso kudu a shekarar 2015 da kuma yanzu da yadda abubuwa suka inganta.

"Matsalata ita ce arewa maso yamma, inda mutane ke kashe junansu da yi wa juna sace-sace.

"Dole na yi musu da tsauri kuma zan ci gaba da zama mai tsauri har sai mun dawo da su kan hanya, mun daidaita musu sahu," in ji shi.

A ƙarshe Shugaba Buhari ya nemi ƴan Najeriya mazauna Saudiyya da su girmama doka su zama masu bin tsari, kuma "kar su yi duk abin da zai jawo ɓaraka a dangantakar ƙasashen biyu da aka shafe shekaru ana ɗasawa".

Shugaban ƴan Najeriya mazauna Saudiyya, Dr. Abdulkadir Maikudi, ya nemi shugaban da ya taimaka wajen samar da kayayyakin aiki musamman na kimiyya da fasaha a makarantar ƴan Najeriya mai zaman kanta a ƙasar.

Jakadan Najeriya a Saudiyya Ambasada Yahaya Lawal da babban jami'in ofishin jakadancin na Jiddah, Ambasada Abdulkarim Mansur, sun bayar da shaida kan kyawun halin kusan mutum miliyan 1.5 ƴan Najeriya da ke can.

"Ƴan Najeriya ƙwararru suna abin kirki kuma suna halayya ta gari da ke nuna ƙimar ƙasarsu," in ji jakadun.