Dauda Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nake yi wa Buhari waka

Bayanan bidiyo, Dalilin da ya sa nake yi wa Buhari waka - Rarara

Latsa hoton sama domin kallon hirar da BBC ta yi da Rarara

Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara ya ce gaskiyar Buhari ce ya sa yake yi wa shugaban na Najeriya waka.

Rarara ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi ta musamman da BBC, inda yake cewa tun yana yaro ake nusantar da shi kan gaskiya da amanar Buhari kuma har yanzu da ya taso ya gani.

Dauda ya kara da cewa burin da Buhari yake da shi na gyara Najeriya da ayyukan da yake yi a yanzu ba za su kirgu ba.

Ko da yake a yanzu ya ce yana dab da sakin wasu wakoki da za su bayyana irin ayyukan da Shugaba Buhari yake yi da wadanda ya kammala, wanda a cewarsa "mutane za su gamsu da ceton Najeriya da Buhari ke yunkurin yi."

Rarara wanda ya karɓi kuɗin wasu ƴan Najeriya don rera wa Buhari waƙa, kuma har yanzu bai saki waƙar ba, ya ce idan da ƴan Najeriya za su karɓi ra'ayinsa da sun bari gwanin nasa ya zarce ya ƙara shekara biyar kan mulki - "don ya kammala ayyukan da ya fara."

Mawaƙin siyasar ya ce ba daɗewa ba zai saki wasu waƙoƙi guda uku kan ayyukan Buhari.

Sai dai bai bayyana lokacin da zai saki waƙoƙin ba, ciki har da wadda ya kira mai taken "shidan Buhari ta fi sha shidan gangan"

Duk da shugaba Buhari na dab da kammala wa'adin mulkinsa amma Rarara ya ce bai san lokacin da zai daina yi wa shugaban waƙa ba.

Rarara ya ce ya yi wa Buhari waƙa 68, kuma a cewarsa bai sa yawan adadin wakokin da ya yi ba a rayuwarsa.

"Amma yanzu mun fara hada kan wakokin da na yi baki daya," in ji shi.

Ban taba rubuta wakar Buhari ba

Rarara

Asalin hoton, Rarara

A cewar Rarara: "Yawancin wakokin da nake yi wa Buhari suna zuwa ne daidai da lokaci, ba wai zama nake na rubuta waka akan shi ba.

"Misali ai na yi wakar Masu gudu su gudu na yi ta lokacin da Buhari ya ci mulki, a lokacin ana maganar idan PDP ta ci mulki sai dai mu gudu mu bar Najeriya.

"To Buhari ya ci mulki muma sai muka mayar da marta ni, a wakar, muka ce in kasan ka yi sata ka gudu.

Rarara ya ce a haka aka yi wakar 'Ga Buhari ya dawo'lokacin Shugaban kasa ya yi rashin lafiya ya je Landan sai aka yi sa a ya ji sauki zai dawo, to a wannan lokacin cikin dare aka yi waƙar da aka ce washegari zai dawo, gaskiya ba na rubuta wakokin Buhari."

Dalilin karɓar kudin ƴan Najeriya don yi wa Buhari waƙa?

Mawaki Dauka Kahutu Rarara wanda aka haifa a Danja da ke jihar Katsina

Asalin hoton, Rara Multimedia

Rarara fashewa ya yi da dariya lokacin da aka yi masa wannan tambaya, inda ya ce mun yi kokarin tabbatar wa da masu cewa farin jnin Buhari ya dushe.

Talakawa sun amsa kira domin kuwa sun tara kudade masu yawa, in ji mawakin, amma bai fadi nawa aka tara ba.

Ya ce wakar da ya karbi kudin ƴan Najeriya tana nan fitowa ba da dadewa ba cikin wakokin da ya yi kan ayyukan Buhari.

Rarara ya ce ya taba kin karbar naira miliyan 500 don ya daina yi wa Buhari waka.

"An taba ba ni naira miliyan 500 domin na daina yi wa Buhari waka amma na ki karba, saboda duk abin da nake yi ina yi ne domin kasata".

Ya ce an sha ba shi kudi domin ya hakura da tafiyar Buhari amma a cewarsa bai taba sa shi jin ya yi gezau ba.

"Babban burina na ga ƙasata ta gyaru kamar yadda sauran kasashen duniya suke, kama daga ci gabanta da habbakarta, yaranmu idan sun zo su rika yin alfahari da ita, in ji mawakin.