Waƙoƙin Hausa 10 da suka fi fice a cikin shekarar 2020
Daga Ibrahim Sheme da Abba Muhammad

Asalin hoton, Hamisu Breaker
Kamar kowace shekara a 'yan shekarun nan, mun duba fagen waƙoƙin Hausa mun ga cewa babu wani abu da ya sauya daga dannewar da waƙoƙin zamani suka yi wa na gargajiya.
Duk da yake akwai ɗaiɗaikun mawaƙan gargajiya da suka fitar da sababbin waƙoƙi, irin su Alhaji Musa Ɗanbade, har yanzu dai mawaƙan zamani masu amfani da fiyano su ne ake yayi.
Sannan wani abin lura shi ne manhajar YouTube ta kasance wani babban ma'auni na gane waƙar da aka fi kallo ko saurare, musamman bayan an ɗora bidiyon ta a intanet.
Ta hanyar lissafi da YouTube, da tattaunawa da su kansu mawaƙan da masu saurare da masu sayar da waƙoƙi da kuma ma'aikatan rediyo, mun gano waƙoƙi 10 da suka yi wa saura zarra a wajen fice a wannan shekara ta 2020 da ta zo ƙarshe.
Ga su ɗaya bayan ɗaya kamar haka:
1. 'Jaruma' - HAMISU BREAKER ƊORAYI
'Jaruma' ce waƙa mafi fice da jan hankali a cikin wannan shekara ta 2020. Fitaccen matashin mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi ne ya rera ta shi kaɗai ba tare da muryar mace ba kamar yadda yawancin waƙoƙin masana'antar finafinai ta Kannywood suke.
Mawaƙin ya yi amfani da kalamai masu ratsa zuciyar masoya, kuma ya nuna ƙwarewa wurin tsara kalaman da dole duk wani masoyi da ya ji waƙar sai ta shiga ransa.
Saboda mamayar da waƙar ta yi a bana, yawancin mutane ba su san cewar Hamisu Breaker ya yi ta ne tun a cikin shekarar da ta gabata ba, wato 2019.
Ba ta yi fice ba ne har sai lokacin da guntayen bidiyoyin wasu matan aure suna rawar waƙar a gaban mazajensu a falukan gidajensu cikin shauƙin ƙauna, suka fara yawo a soshiyal midiya da wayoyin mutane.
Surutun da guntayen bidiyon ya haifar ne ya zaburar da mawaƙin ya yi sauri ya ɗauki bidiyon waƙar, wanda darakta Sanusi Oscar 442 ya bayar da umarni, kuma ana gama aikin bidiyon aka ɗora waƙar a tashar mawaƙin ta YouTube.
Cikin mako ɗaya waƙar ta samu masu kallo miliyan ɗaya a YouTube, wanda ba a taɓa samun wata waƙar Hausa da ta samu masu kallo a cikin ƙanƙanen lokaci irin haka ba.
Abin burgewa game da waƙar shi ne yadda masanin waƙoƙin Hausa Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero, Kano, ya feɗe ta a kan gadon nazari daga farko har ƙarshenta.
Har zuwa yau ɗin nan waƙar 'Jaruma' tana cikin zukatan mutane, domin za ka ji ta ana sanyawa a gidajen rediyo da wajen hira da cikin ababen hawa, kuma ba yaro ba babba.
Ya zuwa yanzu, waƙar ta samu 'yan kallo a YouTube sama da miliyan biyu a cikin wata shida.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a YouTube

2. 'Ciwon Idanuna' - UMAR M. SHAREEF (tare da KHAIRAT ABDULLAHI)

Asalin hoton, Umar M Shareef
A tsawon shekara uku zuwa huɗu waƙar Umar M. Shareef ce mu ke zaɓa a matsayin ta ɗaya a wannan lissafin, to amma a bana waƙarsa mai suna 'Ciwon Idanu Na' ta gusa ta ba 'Jaruma' ta Hamisu Breaker Ɗorayi wannan kujerar, wato dai ta zo ta biyu.
'Ciwon Idanu Na' waƙa ce ta soyayya tsantsa, wadda aka saka ta a cikin fim ɗin 'Ciwon Idanu Na' ta darakta Aminu S. Bono, kuma Abubakar Bashir Maishadda ne furodusan shirin.
Fitaccen mawaƙin shi ya fito a matsayin jarumin fim ɗin tare da Maryuda Yusuf, kuma suka hau waƙar.
Umar M. Shareef ya rera waƙar ne tare da zabiyar da ya fi yin waƙoƙin sa da ita, wato Khairat Abdullahi.
Umar da Khairat sun nuna ƙwarewa wajen zuba kalaman soyayya da shauƙi, wanda hakan ya taimaka wa waƙar wajen samun fice a soshiyal midiya, musamman a wajen matasa. Ita ce kuma waƙar da ƙananan yara suke rera ta tamkar su ne su ka ƙirƙiro ta.
Waƙar 'Ciwon Idanu Na' ta samu masu kallo sama da miliyan biyu a tashar Umar M. Shareef ta YouTube a cikin wata takwas, wanda hakan ya sa ita ce ke bin 'Jaruma' ta Hamisu Breaker Ɗorayi.

3. 'Sambisa' - SANI LIYA-LIYA

Asalin hoton, Sani Liya-Liya
Wannan waƙa ba ta fim ba ce. Ta zo da wani salo wanda ba a saba ganin mawaƙan wannan zamanin na yi ba.
Sani Liya-Liya ya yi ta ne da salon barkwanci. Ya daɗe a fagen waƙa, amma sai a wannan waƙar ne ya yi suna.
Jarumai Ibrahim Yamu Baba da Zainab Sambisa su ne suka hau waƙar a fim ɗin inda aka ga Zainab ta zo hutu a karkara, inda daga saukar ta a mota shi kuma ya fara bin ta a matsayin yana son ta da aure, ita kuma ta bayyana masa cewa gidansu a dajin Sambisa yake, wato inda 'yan ƙungiyar Boko Haram su ke, shi kuma ya ce ba zai je Sambisa ba.
Daga nan ta koma ta na lallaɓar sa, amma dai ya nace a kan ba zai yiwu ba.
Waƙar ta na nishaɗantar da jama'a, musamman irin yadda aka ɗauke ta cikin barkwanci da kuma irin kalaman da mawaƙin ya yi amfani da su. Tabbas, mawaƙin ya nuna ƙwarewa wurin zubo kalmomi masu bada dariya da nishaɗi.
Waƙar ta yi fice ne saboda yawan saka ta da tashar talbijin ta Arewa24 ta ke yi a kullum. Haka kuma ta samu 'yan kallo sama da miliyan ɗaya da rabi a YouTube.

4. 'I Love You' - USMAN SOJABOY

Asalin hoton, Usman Soja Boy
Waƙar 'I Love You' ta Usman Sojaboy ce kan gaba a bana cikin rukunin waƙoƙin Hip-hop na Hausa.
Waƙar ta yi fice a daidai lokacin da mawaƙin suke wani shiri mai suna '90 Days Fiancee' tare da wata Baturiya da ya aura mai suna Lisa.
Wannan waƙa ta yi fice musamman a wurin Turawa, da yake cikin harshen Turanci ya rera ta amma ya ɗan saka Hausa a ciki. Sai dai ba tare da ita matar tasa ya hau waƙar a bidiyon ba.
Daga ƙasashe da dama mutane sun ta yin guntayen bidiyo da waƙar, suna sakawa a shafukansu na sada zumunci tare da masoyansu, kamar yadda aka yi wa waƙar Hamisu Breaker ko yadda aka riƙa yi wa waƙar nan ta 'Jerusalem' wadda mawaƙan ƙasar Kenya Master KG da Nomcebo su ka yi a bana.
Sojaboy ya yi waƙar tasa ne ya na sanar da matar tasa irin son da ya ke yi mata, yana faɗa mata cewar duk abin da ta ke so zai yi mata, ciki har da addu'a, kuma za su kasance tare har abada.
Sai dai kuma duk da wannan waƙa da Sojaboy ya yi wa Lisa, a ƙarshe sun rabu.
Amma duk da haka har yanzu waƙar na ƙara samun masoya, musamman a YouTube inda ta samu sama da 'yan kallo miliyan ɗaya.

5. 'Da So Samu Ne' - DJ AB, DEEZELL, TEESWAG, MR. KEBZEE, LIL PRINCE, GEEBOY, JIGSWAG, MARSHALL, FREEIZIEY, da ZAYN AFRICA

Asalin hoton, DJ AB
'Da So Samu Ne' waƙa ce ta haɗakar wasu fitattun mawaƙan Hip-hop na Hausa mazauna Kaduna, waɗanda sun yi suna matuƙa wajen yin irin wannan haɗakar, kuma a duk lokacin da su ka yi irin wannan taron dangin sai waƙar su ta karaɗe ko'ina.
DJ AB shi ne jagoran waƙar. A bidiyon waƙar an nuno shi a tsakiyar sauran mawaƙan, yana faɗa masu cewar ya haɗa wani kiɗa wanda da so samu ne su yi amfani da shi yanzu.
A nan take aka tada waƙa, inda kowanne daga cikin su ya ke fitowa ya faɗi ra'ayinsa a kan da so samu ne ya samu abu kaza, su kuma sauran sai su tambaye shi in kuma ya samu fa, sai ya ce masu ga abin da zai yi.
Waƙar ta nishaɗantar da jama'a sosai, musamman yadda matasa suka samu salo don zolayar junansu da suke yi da 'da so samu ne!'
Wasu daga cikin jaruman barkwanci ma sun yi amfani da wannan waƙar a cikin irin guntayen bidiyon da su ke saki a tashoshin su na YouTube, kamar irin su Kamal Aboki da sauran su.

6. 'Shalele Na' - ABDUL D. ONE

Asalin hoton, Abdul One
Fitaccen matashin mawaƙi Abdul D. One, wanda tauraronsa ke haskawa a cikin matasan mawaƙa, a wannan karon ya ƙera waƙar soyayya mai suna 'Shalele Na', kuma babu muryar mace a cikin ta.
Waƙa ce mai sanyaya zuciyar masoya, wanda ya sa masoya ke matuƙar son ta, musamman mata.
Mawaƙin ya zazzaga kalaman soyayya da ya ke nuna cewa ya yi wa masoyiyar sa ne.
Waƙar ta yi tasiri a wajen masoya. Duk macen da ta saurare ta, in har ta fahimci kalaman mawaƙin, to, za ta samu sanyin zuciya a kan soyayyar ta, domin waƙa ce mai ratsa zuciya.

7. 'Makullin Zuciya' - UMAR MB (tare da KHAIRAT ABDULLAHI)

Asalin hoton, Umar MB
Umar MB fitaccen makaɗi ne wanda ya rikiɗe ya fara waƙa. A yau, ya na ɗaya daga cikin mawaƙan da ke tashe a ɓangaren kiɗa da waƙa.
Waƙarsa ta 'Makullin Zuciya' ita ce mafi shahara a cikin waƙoƙin sa a wannan shekarar.
Fitaccen jarumi Adam A. Zango da jaruma Zulaihat Abdullahi (ZPreety) su ne suka hau waƙar, inda Saifullahi Safzor ya bada umarni.
Waƙar ta shiga ran mutane ne saboda irin aikin da aka yi wa bidiyonta, domin jaruman sun ba waƙar haƙƙin ta.
Har wani irin sabon salon rawa aka yi wanda ya ke bin kalaman amshin waƙar.
Umar da Khairat sun zuba kalaman soyayya masu daɗi ta yadda dole idan ka saurari waƙar sai ka sake sauraren ta.

8 'Ɗan Alewa' - KHAIRAT ABDULLAHI

Asalin hoton, Khairat Abdullahi
Khairat Abdullahi mawaƙiya ce wadda tauraron ta ke haskawa a fagen waƙa fiye da kowace zabiya a yau. Kusan dukkan waƙoƙin Umar M. Shariff tare da ita ya ke yin su, wato irin su 'Rariya' da 'Mariya'.
A bana, Khairat ta maida hankali wajen shirya waƙoƙi nata na ƙashin kan ta, kuma ta yi su da dama.
A wannan karon sai ta canza salo inda ta ɗauko wata tsohuwar waƙa ta wata mawaƙiya mai suna Atine Jibo wadda ta yi tashe kusan shekara 25 da su ka gabata, ta zamanantar da ita. Sunan waƙar 'Ɗan Alewa'.
Da dama matasa 'yan ƙasa da shekara 25 ba su san waƙoƙin Atine Jibo ba.
Khairat ta yi amfani da basira wajen zamanantar da waƙar, musamman yadda ta ɗauki salon waƙar babu canji, kamar waccan mawaƙiyar ce ta sake rera waƙar.
Jama'a sun yi mamakin yadda zabiyar ta jero wasu daga cikin jihohin Arewa, kuma ta sako irin abincin da su ke ci. Da dama sun so waƙar ta Khairat domin ta tuno masu da waccan tsohuwar waƙar, waɗanda kuma ba su san waƙar ba sai su ji wani sabon abu ne Khairat ta zo da shi.

9. 'Dogara Ya Dawo' - DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA)

Asalin hoton, Rarara
Fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu (Rarara) ya yi waƙar 'Dogara Ya Dawo' ne bayan tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Honarabul Yakubu Dogara, ya koma jam'iyyar APC.
Mawaƙin ya saka gasar rawa, inda duk wanda ya shirya rawa da waƙar zai tura shafinsa na Instagram, sannan ya haɗa da shafin Ali Nuhu da Abubakar Bashir Maishadda, daga nan kuma har zuwa lokacin da aka saka za a gama gasar.
Matasa maza da mata sun yi ta tura rawar da suka yi da waƙar.
Da lokacin da aka sa ya yi, an zaɓi 20 daga cikin bidiyoyin waƙar, daga nan aka tantance har aka samu na 1, na 2 da na 3.
Amma su kansu sauran - wato daga na 4 har zuwa na 20 - ba a bar su haka nan ba, domin mawaƙin ya ba su kyautar kuɗaɗe ta hannun Ali Nuhu, wanda shi ya tura wa dukkan waɗanda suka lashe gasar kuɗinsu ta banki.
Wannan ya sa waƙar ta yi fice.

10. 'Saƙo Ga Shugaban Ƙasa' - SULAIMAN A. TIJJANI (FARFESAN WAƘA) da IBRAHIM YALA

Asalin hoton, Sulaiman Farfesa da Ibrahim Yala
Sulaiman A. Tijjani, wanda aka fi sani da suna Farfesa, tare da fitaccen mawaƙin siyasa Ibrahim Yala, sun yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari waƙa mai suna 'Wasiƙa Ga Shugaban Ƙasa' da salon tambayar shugaban me ya ke jira ne.
Sun nuna irin soyayyar da 'yan Arewa suke nuna masa, amma kuma sun ji shiru.
Mawaƙan sun zazzaga kalmomi masu ma'ana a waƙar, wanda duk wanda ya saurare ta zai gane abin da su ke nufi.
'Yan Arewa da dama sun yi na'am da wannan waƙa saboda irin halin ƙunci da ake ciki.
Waƙar ta yi fice ne a lokacin da mutane ke kulle a gidajensu saboda dokar hana fita ta cutar korona.
A wannan lokacin, musamman dattijai, sun fi sauraron waƙar domin ta ɗebe masu kewa.
A ganinsu, dukkan abin da ya kamata a tunasar da shugaban ƙasa a kansa, an faɗa a wannan waƙar.












