Hamisu Breaker: Waƙar Jarumar Mata ce ta 6 da aka fi kallo a Youtube a Najeriya

Hamisu Breaker

Asalin hoton, Breaker IG

Bayanan hoto, 'Idan zan yi waka ba na tunanin samari da 'yan mata kawai'
Lokacin karatu: Minti 3

Shaharraiyar waƙar nan da ta sa matan aure rawa a lokacin bukuwan ƙaramar sallah ita ce ta zamo ta shida aka fi kallo a Youtube a wannan makon a Najeriya.

Shafin TurnTable Charts na Tuwita ne ya fitar da jadawalin waƙoƙi 10 da aka fi kalla a YouTube a Najeriya a makon da ya gabata, inda aka kalli Jarumar Mata sau 74,900 cikin mako ɗaya kacal.

twitter

Asalin hoton, Twitter

Ga jerin waƙoƙin kamar haka:

  • Cardi B & Megan Thee Stallion - WAP; 393k
  • Simi - Duduke; 86.2k
  • Laycon - Fierce (ft. Reminisce & Chinko Ekun; 84.9k
  • 2Baba ft. Wizkid - Opo; 84.8k
  • Dj Tunez ft. Wizkid - Cool Me Down;
  • Hamisu Breaker - Jaruma; 74.9k
  • Omah Lay - Lo Lo; 71.1k
  • Beyonce, Shatta Wale & Major Lazer - ALREADY; 68.4k
  • Fireboy DML - Tattoo; 62.1k
  • Peruzzi - Lagbaja; 60.2k

Wakar Jarumar Mata dai na ci gaba da jan zarenta a Najeriya saboda irin ɗumbin farin jini da ta yi tun bayan gasar rawarta da wasu matan auren suka yi.

Hamisu Breaker ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, "Sai godiya,'' yana mai nuna farin cikinsa kan wannan nasara da waƙarsa ta samu.

Su ma wasu ƴan masana'antar Kannywood suka taya shi murna a shafukan sada zumuntarsu.

Kauce wa Instagram, 1
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

Ali Nuhu ya ce: ''Ina taya ka murnar Hamisu Breaker Ɗorayi, wannan babbar nasara ce.''

Kauce wa Instagram, 2
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2

Kauce wa Instagram, 3
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 3

Waƙar Hamisu Breaker ce kawai ta Hausa da ta shiga wannan jeri na guda 10 da aka fi kallo a YouTube a makon da ya gabata, kuma mafi yawan waɗanda suka kalle ta daga arewacin ƙasar ne.

Waiwaye

Tun bayan da bidiyon gasar rawar matan aure ya zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya da aka yi lokacin bikin sallah, sai hankalin mutane ya koma kan wakar da ta sa suka taka rawar.

Wannan waka dai takenta shi ne 'Jarumar Mata' wadda Hamisu Breaker Dorayi ya rera.

Duk da cewa mawakin ya ce ya yi wakar ne a karshen shekarar 2019, kuma ya sake ta a farkon 2020, za a iya cewa dubban mutane ba su san ta ba sai a makon bikin karamar sallah, bayan da wasu matan aure suka yi yayin yin rawarta.

A wata hirar bidiyo kai tsaye da BBC Hausa ta yi da Hamisu Breaker a shafinta na Instagram, matashin mawakin ya ce wannan gasa da mata suka yi ba karamin farin jini ta kara masa shi da wakar ba.

Ya ce: ''Wakar ta yi matukar tashe a lokacin da ta fito amma na yi tunanin ma tashenta ya dan ja baya, kawai kwanan nan sai na ji ta sake karade duniya.''

'Abin da ya sa na yi wakar'

Breaker ya ce bai san adadin mutanen da suka kira shi a waya don sanar da shi cewa ya ga yadda wakarsa ta yi tashe a wannan dan tsakanin na bikin sallah ba.

BBC ta tambaye shi kan ra'ayinsa kan rawar matan aure a bidiyo a saka a shafukan sada zumunta.

Sai ya ce duk da dai a tunaninsa sanya rawar a social media din na iya zama kuskure. Amma tun da ni ba malamin addini ba ne ba zan iya fashin baki kan hakan ba.

Hamisu Breaker

Asalin hoton, Chizo Photography

Bayanan hoto, An haifi shahararren mawakin Hausan ne a shekarar 1993 a Kano

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta