Coronavirus: Wakoki 10 da ke debe wa mutane kewa a lokacin kulle

Billie Eilish

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, James Fitzgerald
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Minute
  • Lokacin karatu: Minti 5

A lokacin da kusan rabin al'ummar duniya ke rayuwa karkashin dokokin kulle da barin tazara, da yawa daga cikinmu na neman wakokin da za su debe mana kewa.

Suna taimaka mana mu nutsu ko mu yi alhini ko ma mu taka rawa yayin da muke bin dokokin zaman gida.

Tawagar Minti Daya Da BBC - wadda ke samar da labarai sa'a 24 duk rana ga gidajen rediyo a fadin duniya - na ganin cewa za a iya shawo kan ko wane kalubale tare da wakokin da suka dace.

Da alama gidajen rediyon da muke kawance da su a birane 100 a kasashe 40 na ganin haka.

Mun tambayi wasu daga cikin masu gabatar da shirye-shiryen a wadanann tashoshin wakokin da suke sawa masu sauraronsu don debe masu kewa a lokacin wannan annoba.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

1. Wakar Bop daddy ta Falz wadda Ronke ta tashar rediyon Splash FM a birnin Ibadan, Najeriya ta zaba

Ronke

Asalin hoton, Ronke Giwa Onafuwa

'Yan Najeriya da dama na kewar zuwa gidajen rawa yanzu, a cewar Ronke. Shi ya sa suka kirkiri gasar #BopDaddyChallenge da ake ta yadawa musamman a shafin TikTok.

Wadanda suka saba zuwa gidan rawa a baya, yanzu sai dai su shiga shafukan sada zumunta. "Sai su yi kwalliya kamar za su fita amma babu inda za su!" ta bayyana mana tana dariya.

"Wakar ba ta da wata ma'ana amma kidan na da matukar dadi mutum ya yi rawa a gida da shi."

Kauce wa YouTube, 1
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 1

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

2. Wakar Everything I Wanted ta Billie Eilish wadda Tebogo na tashar rediyon Gabz FM a birnin Gaborone, Botswana ya zaba

Tebogo

Asalin hoton, Tebogo Mokoto

Wakar Billie Eillish mai ban tausayi na magana ne kan wani mugun mafarki da ta yi inda ta kashe kanta - amma babu wanda ya damu.

Ba waka ce da za a yi wa rawa ba amma mai gabatar da shirye-shirye Tebogo ya ce waka ce da ya kamata a ji a wannan lokaci, abin da ya sa tashar Gabz FM ke yawan sa wa masu saurarensu.

"Tana nuna halin da ake ciki a Botswana yanzu," a cewarsa.''

Kauce wa YouTube, 2
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 2

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

3. Wakar Imagine ta John Lennon wadda Michael na tashar Metro Plus a Hong Kong ya zaba

Michael

Asalin hoton, Michael Vincent

Shaharraiyar wakar John Lennon na kira da a yi hadin kai da son juna. Kuma Michael na tashar Metro Plus a Hong Kong na ganin al'ummar Hong Kong a yanzu na nuna soyayya ga juna fiye da a baya.

"Sai ka ga mutum a bakin titi ba tare da takunkumin rufe fuska ba, kuma wani ya taimaka masa.

Ba lallai ma su kalli mutumin ba amma za su taimaka masa," a cewarsa.

Kauce wa YouTube, 3
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 3

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

4. Wakar Mulk Kay Nojawano ta gargajiya wadda Asfandyar na tashar rediyon Power 99 a birnin Islamabad, a Pakistan ya zaba

Asfandyar

Asalin hoton, Asfandyar Alam

Aikin Asfandyar mai wahala shi ne samar da fage mai dauke damuwa a tasharsu a lokacin annobar.

Tawagarsa ta zabi ta sauya wata wakar gargajiya wadda ke kara wa mutane kwarin gwiwa.

"Wakar tana sawa su ji kamar mayaka. Kamar dakaru. Me ya sa? Saboda suna zaune a gida, suna kare lafiyarsu da ta iyalinsu."

Kauce wa YouTube, 4
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 4

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

5. Wakar Par Pira ta BeePee wadda Okeng na tashar rediyon King a birnin Gulu na Uganda ya zaba

Okeng

Asalin hoton, Radio King

Dokar kullen nan ta kara wa rediyo muhimmanci fiye da a baya a kauyukan arewacin Uganda.

Shirin Safe da ake yi a tashar Okeng na da bangare da ake kiran mutane biyu da ke son su sadu da juna amma ba su da kati a wayarsu.

Haka kuma ana soyayya da juna ta rediyo, masoya matasa a Gulu na amfani da rediyo ta hanyar neman a sa masu wakar soyayya da wani mawakin yankin BeePee ya yi.

Okeng ya ce "Wakar na nufin, 'ki sa ni a ranki a lokutan farin ciki da na bakin ciki''.

Kauce wa YouTube, 5
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 5

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

6.Wakokin Quarantine Show ta Dubioza Kolektive wadda Naida ta gidan rediyon Antena a birnin Sarajevo da ke Bosnia da Herzegovina ta zaba

Naida

Asalin hoton, Purple Key Agency

Saboda karuwar mutane a intanet, wasu daga cikinmu na farin ciki su yi waya da abokansu ta manhajar Skype ba tare da wata matsala ba.

Amma abin mamaki, mambobin kungiyar mawaka ta Dubioza Kolektiv bakwai na iya amfani da hanyar kiran waya ta bidiyo su rera wakoki daga gida.

Gidan rediyo na Antena na son zaba daga wakokin nan da suke yi daga gida kai tsaye. "Ku wanke hannuwanku!" a cewar wakar mai dadin gaske.

Kauce wa YouTube, 6
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 6

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

7. Wakar Resistire 2020 ta David Bisbal wadda Vanesa Martin da Alex Ubago da wasu wadda Valeria daga Tashar Metropolis FM a birnin Montevideo da ke Uruguay ta zaba

Valeria

Asalin hoton, Valeria Oddone

An yi wakar asali a shekarar 1988, wakar Resistire ta sake bayyana a matsayin sauti mai nuna jajircewa a lokacin da mazauna Sifaniya suka rika rera ta daga gidajensu, bayan cutar korona ta mamaye kasar.

Ana yawan bukatarta a gidajen rediyo a Uruguay bayan da wasu manyan mawaka suka sake rera ta a 2020.

Har yanzu cutar ba ta yi yawa a Uruaguay ba, in ji Valeria, amma mutanen kasar na kallon sauran kasashen duniya cike da fargaba.

Kauce wa YouTube, 7
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 7

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

8. Wakar Ride Natty Ride ta Bob Marley wadda Maya ta gidan Rediyon Capital a Khartoum, Sudan ta zaba

Maya

Asalin hoton, Maya Gadir

Maya na son wakokin Bob Marley. Tana ganin cewa suna nufin kowa na da ranarsa.

Masu zanga-zanga da ke kira a kawo sauyi a Sudan a 2019 sun mayar da shaharraren mawakin Reggae ya zama "alama ta 'yanci" kuma wannan tunanin ya ci gaba har bayan shekara guda.

Maya ta ce tana ci gaba da buga wakar Marley, "ba a matsayin muryar juyin juya hali ba, amma a matsayin uba mai kwantar da hankali, wanda ke cewa, 'za ku yi nasara a wannan'".

Kauce wa YouTube, 8
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 8

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

9. We Will Rock You ta Queen wadda Moustafa na gidan rediyon Radio One a Bagadaza, Iraki ya zaba

Moustafa

Asalin hoton, Moustafa Ahmed

"Wannan takenmu ne," in ji Moustafa, game da wannan wakar da ta yi tashe a shekarun 1970.

"Duk lokacin da muka fuskanci wani kalubale a tasharmu, akwai abin da muke cewa: "Za mu haye wannan siradin; wannan ba matsala ba ce gare mu.

''Haka ma masu saurarenmu. Duk lokacin da suke jin ba dadi, ai su bukaci mu sa masu wakar We Will Rock You."

Ga Moustapha, dokar zaman gida wata shaida ce ta cewa rediyo na samar wa matasa 'yan Iraki wata kafar yaye damuwarsu ta yau da kullum.

Kauce wa YouTube, 9
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 9

Presentational white space
Short presentational grey line (transparent padding)

10. Wakar Rumah Kita ta God Bless wadda Hisa ta tashar Rediyon Smart FM a birnin Jakarta a Indonesiya ta zaba

Hisa

Asalin hoton, Hisa Audrina Ginting

Fassararta- Gidanmu. Wannan sautin ya samu sabuwar ma'ana a gidan rediyon Smart Fm na Jakarta.

Mai gabatar da shirye-shirye Hisa na sanya wa masu saurarenta da ke watsi da dokar barin tazara.

"Muna so mu gayyace su, su zauna a gida su bi dokoki, "in ji ta.

"Sakon da wakar ke isarwa shi ne yadda Indonesia ta ke kasa mai girma; duk inda ka je a fadin duniya, nan ne gida.

''Kuma a yanzu, abin da ya fi dacewa shi ne mu zauna a Indonesiya kuma a nan din ma a cikin gidajenmu."