Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Asusun IMF ke tsoma baki cikin harkokin Najeriya?
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
A baya-bayan nan ne Asusun Lamuni na Duniya IMF ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta tsara ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi da zai ba ta dama ta iya biyan mafi ƙanƙantar albashi da ma’aikata suka nema.
IMF ya bayar da shawarar ce a rahoton da ya fitar a ƴan kwanakin nan.
Asusun lamunin na duniya ya ce ya bayar da shawarar ce saboda kuɗin mafi ƙanƙantar albashin da ake tattaunawa a kai ya fi karfin abin da aka ware masa a kasafin kuɗin 2024.
Wannan dai ba shi ne karon farko da IMF ke bai wa gwamnatin Najeriya shawara kan yadda yake ganin ita gwamnatin za ta bi domin samun maslaha a al'amuran da suka shafi tattalin arzikinta ba.
Misali na baya-bayan nan shi ne yadda IMF ɗin ya shawarci gwamnati ta janye tallafin wutar lantarki, wanda kuma gwamnatin ta yi ta hanyar ƙara kuɗin wuta ga rukunin waɗanda suka fi kowa samun wuta a Najeriya.
Haka kuma IMF tun da daɗewa ya yi ta bai wa Najeriya shawarar ta daina biyan tallafin man fetur, kuma shugaba Bola Tinubu ya aiwatar jim kaɗan bayan hawansa kan mulki.
A mafi yawan lokuta, al'ummar Najeriya na kokawa kan irin shawarwarin da ba sa yi wa talaka daɗi kuma hakan ne ya sa mutane suka soma neman sanin alaƙar IMF da Najeriya kuma me ya sa yake yin uwa da makarɓiya a tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.
Kan haka ne muka tuntuɓi Farfesa Kabiru Isa Dandago, masani kan tattalin arzikin Najeriya da ke koyarwa a jami'ar Bayero da ke Kano domin jin amsoshin tambayoyin da ma wasu.
Mene ne aikin IMF a duniya?
An kafa asusun IMF ne a watan Yulin 1944, lokacin wani taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya mai suna Bretton Woods Confrence.
Yanzu haka asusun mai hedikwata a birnin Washington na Amurka na da ƙasashe 190 a matsayin mambobi.
Farfesa Kabiru Isa Ɗandago ya bayyana irin ayyuka da alhakin da suka rataya a wuyan asusun lamunin na duniya wato IMF, kamar haka:
"Asusu ne da ke sarrafa harkokin kuɗi na duniya da ƙasashen duniya suka kafa domin ya riƙa bayar da shawarwari kan yadda za a inganta harkokin manufofin kuɗi da kuma taimaka wa ƙasashen da suke mambobinta da gudunmawa ta hanyar kyauta ko bashi domin su inganta ɓangarori daban daban na tattalin arzikin ƙasashen da suke cikinta." In ji Farfesa Ɗandago.
IMF, a cewarsa, "na da manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziki da ke mara masa baya da kuma zuba kuɗi sosai a ciki domin a yi amfani da kuɗin wajen taimaka wa ƙasashe masu tasowa ta yadda za su inganta tattalin arzikinsu ko dai ta hanyar ba su bashi da za su riƙa biya a hankali ko kuma ba su gudunmawar kuɗi 'grant' ba a matsayin bashi ba."
Alaƙar IMF da Najeriya
A cewar masanin, Najeriya mamba ce ta IMF kuma tana da damar neman gudunmawa daga ƙungiyar ko ta hanyar bashi ko kuma kyauta.
"Sannan kowace mamba tana biyan kuɗin kasancewa a asusun wato 'Participation Fee', in ji Fafesa Dandago.
Ya ce Najeriya na cikin na gaba-gaba a Afirka, da ke biyan wannan kuɗi, "don haka idan Najeriya tana da matsalar kuɗi da za ta yi wasu ayyuka, sai ta ruga wajen IMF ta nemi bashi."
Farfesa Dandago ya bayyana cewa mafi yawan lokaci IMF yana bayar da bashi ya kuma sa wasu ƙa'idoji da ƙasashe za su cika kafin su karɓi bashi da kuma bayan sun karɓi bashin.
"Kasancewar Najeriya mamba ce a asusun na IMF, haƙƙin IMF ne idan Najeriya ta nemi bashi ya ba ta, kuma haƙƙinsa ne ya nuna wa Najeriya yadda za ta riƙa biyan bashin a kai a kai ba tare da an samu tangarɗa ba.
Shi ya sa idan suka bayar da bashin nan ko kafin su ba da bashin, za su bai wa Najeriya shawarwari kan yadda za ta guji karɓar bashin,"
"Ko in sun karɓi bashin ya yi nauyi an kasa biya, za su ba su shawara kan yadda za su biya bashin." In ji masanin.
Bugu da ƙari, farfesa Ɗandago ya ƙara da cewa "idan IMF ya bai wa Najeriya bashi kan gina hanyoyi ko gina filin jirgin sama ko gina gadoji, sai kuma Najeriya ta kasa biya, "IMF sai ya sa wasu ƙa'idoji da Najeriya za ta iya biyan bashin."
IMF na iya bayar da shawarar a cire kashi 40 cikin 100 na ma'aikata wanda hakan zai ba su damar yin tattalin kuɗin da ake kashewa wajen biyan ma'aikatan wanda zai taimaka wa ƙasar ta iya sauke nauyin bashin da ta karɓa.
Masanin ya ce Najeriya tana ɗaukar shawarwarin ne domin ta ci gaba da samun bashi daga hannun IMF.
Farfesa Dandago ya ce ko kusa IMF ba katsalandan yake yi wa ƙasashe mambobinsa ba saboda shawarwarin da asusun ke bayarwa na yi ne domin sauƙaƙa wa ƙasashen don su iya biyan bashin da suka karɓa.
"Najeriya ba za ta ci gaba da karɓar kuɗinsa ba ba tare da biyan bashin ba kuma ya yi shiru, a don haka babu maganar katsalandan a nan, aikinsu kawai suke yi." In ji masanin.
IMF da gwamnati take hulɗa...
Game da koken da jama'a suke yi kan yadda mafi yawan shawarwarin da IMF ke bai wa Najeriya ba su da kyakkyawan tasiri ga ci gabansu kuwa, Farfesa Dandago ya ce IMF a kowane lokaci yana hulɗa ne da shugabanni ba da talakan ƙasa ba.
"Ba ruwansu da talakawa, ko suna koke, a wurinsu, talakawan ne suka zaɓi wakilansu da suke tattaunawa da su." kamar yadda Farfesa Dandago ya ce.
Ya kuma ce idan har cikin shawarwarin akwai waɗanda ba su yi wa gwamnati daɗi ba, hukumomin ƙasa na iya zamewa sai dai "hakan zai zo da sakamako".
"Nan gaba idan sun zo suna son a ba su rancen kuɗi ba za su ba da ba, kuma hanyoyin da suke samu na kuɗin nasu da hanyoyin samun kuɗin ba amfani ake da su ba sosai yadda za su iya samun kuɗin da za a yi ayyukan raya ƙasa.
Don haka idan Najeriya ta ce ba za ta bi shawarar IMF ba a halin da take ciki yanzu, za su ƙare ba sa aikin komai sai biyan albashi da kuma wasu ayyuka na tabbatar da cewa akwai jami'an gwamnati suna hada-hada a ƙasa." In ji Farfesa Ɗandago.
Mafita ga gwamnatocin Afirka
Farfesa Dandago ya ce idan har gwamnatocin Afirka ciki har da Najeriya na son fita daga ƙangin yawan karɓar bashi daga hannun IMF, to dole ne su karɓi shawarwarin cikin gida daga masana a Najeriya.
A cewar Farfesan, "Shawarwarin da mu ƴan ƙasa da muka san abin da yake damun mu, da mu da waɗanda suke can ƙasa, amfani da su shi ne zai kawo ci gaban ƙasa, amma shawarwarin asusun lamuni na duniya, IMF da bankin duniya, World Bank, ba yadda za a sa ran za su kawo wani ci gaba a ƙasa, sai dai a yi ta koma baya."
Ya ce shawarwarin na IMF "ba sa tasiri saboda ba shawarwari ne da aka fito da su daga gida ba, shawarwari ne da aka mulmulo daga wasu wurare kuma an mulmulo su don kare muradun waɗanda suke da ƙarfin iko a waɗannan cibiyoyi na kuɗi.
"Suna tunani ne irin nasu, ba su san matsalolinmu na ƙasa ba, idan da za a ce za su ajiye waɗannan abubuwan a bi namu da ke tasowa daga ƙasa, a bi shawarwarin da muke fitowa da su daga gida, shi ne za a samu maslaha a samu ci gaba mai ɗorewa a ƙasa." in ji Farfesa Dandago.