Wane irin ƙarfi China ke da shi a yaƙin kasuwanci da Amurka?

Wani riƙe da wani hoto da ke nuna Trump.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zai yi wuya Washington ta iya kassara China a yaƙin kasuwanci da suke yi
    • Marubuci, Koh Ewe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yaƙin kasuwanci tsakanin ƙasashe biyu mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya a yanzu na ci gaba da yaɗuwa.

Kayayyakin China da ke shiga Amurka na biyan harajin da ya kai kashi 245, inda ita ma Beijing ta mayar da martani ta hanyar laftawa Amurka harajin kashi 125.

Masu saye, sana'o'i da kuma kasuwanni na ci gaba da zama cikin rashin tabbas da kuma fargabar jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali.

Shugaban China Xi Jinping ya sha nanata cewa kofarsu a buɗe take don tattaunawa, sai dai ya yi gargaɗin cewa, idan ta kama, za su iya yin faɗa har sai sun ga abin da ya turewa buzu naɗi.

A nan, mun duba wasu abubuwan da Beijing ke tinkaho da su wajen mayar da martani ga harajin shugaban Amurka Donald Trump.

China za ta iya jure wa

Wani ma'aikaci ke gyara fitilu a wata masana'anta a Yantai.

Asalin hoton, Getty Images

China ita ce ƙasa ta biyu da ta fi girman tattali arziki a duniya, abin da ke nufin za ta iya jure tasirin da ƙarin harajin zai yi, ba kamar sauran ƙananan ƙasashe ba.

Ƙasar mai al'umma sama da biliyan ɗaya, na da girman tattalin arziki da kuma harkokin kasuwanci - waɗanda za su iya tsayawa masu fitar da ƙaya idan suka fara jin tasirin ƙarin harajin.

Har yanzu dai Beijing na ci gaba da fama da jama'arta wadda ba sa kashe kuɗaɗe sosai. Sai dai ƙaruwar abubuwa, kama daga tallafin da ake bai wa na kayayyakin gida zuwa na "jiragen ƙasa ga masu ritaya da ke yin balaguro, hakan na iya canzawa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuma harajin da Trump ya saka ya bai wa jam'iyyar Gurguzu a China ƙwarin gwiwa mai karfi na samar da wasu hanyoyi kasuwanci a ƙasar.

Shugabanni na iya jure zafin da ƙarin harajin zai yi don guje wa yin abin da suka yi imani da cewa mamayar Amurka", kamar yadda Mary Lovely, ƙwararriya kan harkar kasuwanci tsakanin Amurka da China a Cibiyar Peterson da ke Washington DC ta faɗa wa BBC a farkon watan nan.

Har ila yau, ƙasar Sin tana da ƙarfin jure ƙarin harajin a matsayinta na mai mulkin kama-karya, saboda ba ta da damuwa game da ra'ayin jama'a na gajeren lokaci. Babu wani zaɓe da za a yi a nan kusa - wanda kuma zai iya yin alkalanci ga shugabannin ƙasar.

Har yanzu, ana ci gaba da nuna fargaba, musamman saboda an riga an nuna rashin jin daɗi game da matsalar kadarori da kuma rashin ayyuka da ke ci gaba da gudana.

Rashin tabbas kan ƙarin haraji wani cikas ne ga matasa waɗanda ba su taɓa sanin haka ba, illa samun ci gaba a China.

Jam'iyyar ta yi kira ga masu kishin ƙasa da su goyi bayan mayar da martani kan ƙarin harajin da ta yi, inda kafafen yaɗa labarai na gwamnati ke kira ga mutane da su yi jure.

Shugaba Xi Jinping na iya nuna damuwa, sai dai zuwa yanzu, Beijing ta turje da kuma yin kafiya. Wani jami'i ya tabbatar wa ƙasar cewa: "Sama ba za ta faɗo ba."

China ta daɗe tana zuba jari don makomarta

Wani ma'aikaci yana duba wata mota mai amfani da lantarki da aka ƙera.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, China ta bi sahun zamani waje samar da masana'antun zamani daga ƙera motoci masu aiki da lantarki zuwa ƙirƙirarriyar basira (AI)

China ƙasa ce da aka sani a matsayin cibiyar masana'antu ta duniya - sai dai tana zuba biliyoyin kuɗaɗe zuwa masana'antu na zamani.

Karkashin mulkin Xi, China ta kasance tana gasa da Amurka wajen mamaya a ɓangaren fasaha.

Ta zuba ɗimbin jari a fasahar cikin gidanta, daga kayayyakin da ake sabuntawa zuwa ƙiƙirarriyar basira.

Alal misali, sun haɗa da manhajar ƙirƙirarriyar basira (AI) ta DeepSeek wadda aka samar da kuma ake ganin ƴar adawa ce ga manhajar ChatGPT, da kuma kamfanin ƙasar mai ƙera motocin lantarki da ya zarce na Tesla a shekara da ta gabata, wajen zama kamfani mafi girma na ƙera motoci masu amfani da lantarki a duniya.

Kamfanin Apple mai ƙera wayar iPhone na rasa tagomashi a kasuwa zuwa abokan kasuwancinsa na cikin gida kamar Huawei da Vivo.

A baya-bayan nan, Beijing ta sanar da shirin kashe sama da dala tiriliyan ɗaya cikin shekaru goma masu zuwa domin tallafawa ɓangaren ƙere-ƙere na AI.

Kamfanonin Amurka sun yi ƙoƙarin sauya wuraren da suke samar da kayayyaki a China, sai dai sun ƙasa samun irin kayayyakin da suke so da kuma ma'aikatan da ya kamata a wasu wuraren.

Darussa daga ƙarin harajin Trump

Shugaban China Xi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A baya-bayan nan shugaban China Xi (a tsakiya), ya kai ziyarar diflomasiyya zuwa kudu maso gabashin Asiya domin ƙarfafa dangantaka da abokan kasuwanci

Tun a can baya da harajin Trump ya afkawa na'urorin samar da lantarki daga hasken rana na China a 2018, Beijing ta tashi tsaye domin tunƙarar abin da zai je ya dawo daga tsare-tsaren Amurka.

Ta zuba biliyoyin kuɗaɗe a ɓangaren samar da kayayyaki, da kuma ƙarfafa dangantaka da kudancin duniya.

Faɗaɗar hulɗar kasuwanci tsakanin kudu maso gabashin Asiya da yankin Latin Amurka da kuma Afirka, na zuwa ne a daidia lokacin da China ke ƙoƙarin same kanta daga Amurka.

Manoman Amurka sun taɓa samarwa China da waken soya da ya kai na kashi 40 - yanzu ya ragu zuwa kashi 20. Bayan yaƙin kasuwanci na baya, Beijing ta fara noman waken soya a cikin gida, kuma sun sayi irinsa mai yawa a Brazil - wadda a yanzu ta zama wanda ta fi samar da waken suya a duniya.

Yanzu dai ba Amurka ce ƙasar da China ta fi kai kayayyakinta ba: inda ta fi kai su kudancin Asiya. China ta kasance babbar mai hulɗar kasuwanci ga ƙasashe sama da 60 a 2023 - kusan ninki biyu idan aka kwatanta da na Amurka.

Hakan ba yana nufin cewa Amurka, wadda tafi girman tattalin arziki a duniya, ba abokiyar kasuwancin China bane. Sai dai yana nufin cewa Washigton ba za ta takwara China da sauki ba.

Bayan rahotannin da ke cewa fadar White House za ta yi amfani da batun tattaunawar kasuwanci na ƙasashe biyu wajen mayar da China saniyar-ware, Beijing ɗin ta gargaɗi ƙasashe wajen cimma yarjejeniya da Amurka wadda za ta yi daban da muradun China.

Wannan zai zama zaɓi ne da ba zai yiwu ba ga yawancin ƙasashen duniya.

"Ba za mu zaɓa ba, kuma ba za mu taɓa zaɓa ba tsakanin China da Amurka," kamar yadda ministan harkokin kasuwancin Malaysia Tengku Zafrul Aziz ya faɗa wa BBC.

China ta san lokacin da Trump zai saduda

Wani ɗan kasuwa riƙe da waya a hannu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gwamnatin Amurka ta samu kuɗaɗen da yawa cikin ƙanƙanin lokaci bayan da Trump ya sanar da ƙarin haraji kan ƙasashe da yawa

Trump ya cije a daidai lokacin da hannayen jari ke yin ƙasa bayan sanar da ƙarin haraji a farkon watan Afrilu.

Sai dai ya yi amai ya lashe, inda ya dakatar da yawancin harajin da ya ƙara na tsawon kwanaki 90, bayan da suka samu ƙarin kuɗaɗe shiga a kasuwannin hada-hada.

Tuni Trump ya bayyana cewa zai iya rage yaƙin kasuwanci tsakaninsa da China, inda ya ce harajin da aka ƙara wa kayayyakin China "zai ragu, amma ba duka ba".

Don haka, ƙwararru sun nuna cewa yanzu Beijing ta san cewa kasuwar hada-hada za ta saka Trump ya ɗan sassauta.

China na da hannun jari da ya kai dala biliyan 700 a kasuwannin Amurka. Japan ƙawar Amurka, ita ce kaɗai ke da abin da ya zarce hakan.

Wasu sun kalubalanci cewa wannan ya bai wa Beijing dama: kafofin yaɗa labaran China sun sha gabatar da batun sayarwa ko kuma riƙe abubuwan da suke saya daga Amurka da ɗaukar hakan a matsayin wani "makami".

Sai dai ƙwararru sun yi gargaɗin cewa China za ta ɗanɗani kuɗarta kaɗan daga wannan yanayi.

Maimakon haka, hakan zai sa Beijing ta yi asarar hannayen jarinta a kasuwannin hada-hadar Amurka da kuma kawo rashin daidaiton kuɗin ƙasar na yuan.