Sabon salon da ƙungiyoyi za su iya amfani da shi wajen zura ƙwallo

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Alex Keble
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, BBC Sport
- Lokacin karatu: Minti 3
Duk wanda ya kalli gasar Premier League daga 2008 zuwa 2012 zai iya tuna yadda Rory Delap yake jefa ƙwallo a ƙungiyar Stoke City.
Ƙarfin da yake amfani da shi a wajen jefa ƙwallon a ragar abokan karawarsu na firgita ƴan wasan baya.
Ƴan wasan baya sun yi fama da ƙarfi da kuma tashin ƙwallonsa, har ya kai ga mai tsaron ragar Hull City Boaz Myhil ya gwammace ya buga ƙwallo waje domin bai wa Stoke City bugun kwana a kan ya bari ta tafi jifa.
Stoke ta zura ƙwallo 25 cikin shekara huɗu ta hanyar jifa (throw-in) ɗin Delap. Abu ne da kowace ƙungiya za ta iya amfani da shi, amma har yanzu babu wanda ya gwada.
Amma tun daga wannan lokacin da Delap ya yi zamaninsa a Stoke, ƙungiyoyin ba su cika amfani da jifa wajen samun damar zura ƙwallo ba.
Delap ya nuna yadda za a iya amfani da throw-in. Amma akwai yadda za a iya ɗorawa saboda throw-in ɗin dama ce da ba a busa offside kuma ba a busa fawul saboda mai jifar ya yi amfani da hannu.
Kimanin sau 35 a kowane wasa ake samun damar jifa, a lokuta da dama kuma ana samu ne a kusa da raga.
Amma ƴan wasan kan su ba su fahimci damar da jifa ke ɗauke da ita ba in da a lokuta da dama ƴan wasa na jefa ƙwallon ne zuwa wani na kusa da su. Wasu na yi wa jifa ma kallon abu marasa muhimmanci a ƙwallo.
'Wulla ƙwallo da ƙarfi kusa da raga'

Asalin hoton, Getty Images
Na farko, ya kamata ƙungiyoyi su fara amfani da wannan salon na Delap wajen wulla ƙwallo da ƙarfi zuwa kusa da raga inda ƴan wasansu za su taru domin sa kai.
Delap dai ya yi wasan Javelin a baya - lamarin da ya ƙara masa ƙarfin iya jefa ƙwallo - amma duk da haka za a iya sa ƴan wasa su shiga atisayen jifa domin ƙara ƙarfin jikinsu sannan za a iya koya musu yadda za su iya jefa ƙwallo da nisa.
Ƙungiya kamar Arsenal na dogara kan bugun ƙusurwa domin zura ƙwallo cikin raga, a baya ma Arteta ya yi farin ciki da aka ce suna ƙwallo kamar Stoke City, idan ta yi amfani da wannan, zai iya ƙara musu damar cin ƙwallo saboda suna da ƴan wasa masu tsayi.
'Yin amfani da damar rashin offside'

Asalin hoton, BBC Sport
Na biyu, idan ƙungiya ta samu jifa da ba a kusa da raga ba ne, ƴan wasa su ruga bayan masu tsaron baya saboda ba za a iya busa satar fage ba, idan da yawan su suka ruga to mai wulla ƙwallon zai samu damar jefa wa mutanen da suka ruga kuma sun je kusa da raga ke nan.
Idan kuka kalli hoton da ke sama, yadda Luis zai iya rugawa bayan ƴan wasan PSG, idan da a ce ɗan wasan Liverpool ya wulla masa ƙwallon, zai iya samun dama kamar yadda aka kwatanta da farin layi.
'Wulla ƙwallo zuwa wani gefen filin'

Asalin hoton, BBC Sport
Ɗan wasan Arsenal mai riƙe da ƙwallon zai iya wulla wa Saka - wanda farin layi ke nunawa - saboda yana wani gefe da babu mutane da yawa, amma ya gwammace ya wulla wa na kusa da shi wanda jan layi ke nuna wa.
Idan an taru kusa da wanda zai jefa ƙwallo, ya kamata mai jefa ƙwallon ya kalli can nesa a ɗayan ɓangaren filin sannan ya wulla masa da ƙarfi. Hakan zai buɗa dama kasancewar da yawan ƴan wasa sun riga sun taru kusa da mai jifa.
A zamanin yanzu ma masu horar da ƴan wasa wajen bugun ƙusurwa da bugun tazara suna yin tashe.
Jifa ba ta da bambanci da bugun ƙusurwa kusa da raga. Me ya sa aka amince da bugun ƙusurwa amma idan mutum ya jefa ƙwallo kusa da raga za a ga kamar rashin ƙwarewa a ƙwallo ne?
Hakan saboda ba a amfani da jifa yadda ya kamata ne. Wanda ya yi yadda ya kamata kuma sai a ga kamar ya saɓa wa doka ne.
Delap ya ƙirƙiri sabon salon jifa a baya - amma ya nuna mana cewa akwai hanyoyi daban na yin amfani da jifa.











