Sabbin shafukan da ke nuna abin da mutane ke aikatawa a ɗakunan otal

    • Marubuci, Wanqing Zhang
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global China Unit and Eye Investigations
  • Lokacin karatu: Minti 7

A wani dare a shekarar 2023, Eric ya gano wani abu da ya girgiza shi a lokacin da yake kallon bidiyo a wani shafin sada zumunta da ya saba amfani da shi wajen kallon abubuwan batsa,.

Eric ya gane cewa mutanen da ke cikin bidiyon batsar da yake kallo shi ne da budurwarsa inda bidiyon ya nuna yadda suke shiga dakin otel, suna sauke kayansu, daga bisani kuma ya nuna lokacin da suke saduwa.

Nan take sai Eric ya fahimci cewa an ɗauke su ne a asirce lokacin da suka kwana a otel din da ke Shenzhen a kudancin China.

Makonni uku kafin hakan, sun kwana a ɗakin otel ɗin ba tare da sanin cewa an boye kyamara a dakin ba. Daga baya sai aka wallafa bidiyon, inda dubban mutane suka kalla a shafin intanet, ciki har da Eric kansa.

A nan ne Eric ya koma daga mai kallon irin waɗannan bidiyo zuwa wanda aka zalunta.

Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da kalamai masu tayar da hankali

Irin wannan ɗaukar bidiyo a asirce ya daɗe yana faruwa a China, tsawon aƙalla shekaru goma, duk da cewa an haramta samarwa da rarraba batsa a kasar.

Amma a shekarun baya-bayan nan, batun ya ƙara ɗaukar hankali a shafukan sada zumunta inda mutane, musamman mata, suke tattaunawa kan dabarun yadda za a gano ƙananan kyamarori da ake boyewa, wasu ma har sun kai ga kafa shingaye a cikin dakunan otel don kauce wa daukar su a asirce.

A watan Afrilun da ya gabata, gwamnati ta fitar da sabbin dokoki da ke wajabta wa masu otel su riƙa binciken dakuna akai-akai don gano kyamarorin da aka ɓoye. Amma duk da hakan, barazanar ba ta gushe ba.

Binciken BBC ya gano cewa har yanzu akwai dubban sabbin bidiyoyin da aka ɗauka a ɗakunan otel, ana sayar da su a matsayin batsa a shafuka da dama.

Yawancin irin waɗannan bidiyon ana tallata su ne ta manhajar aika saƙonni da ta sada zumunta ta Telegram.

A tsawon watanni 18, na gano shafukan intanet da manhajoji guda shida da ake yaɗa su a Telegram. Dukkaninsu sun yi iƙirarin cewa suna sarrafa kyamarori sama da 180 da aka ɓoye a ɗakunan otel, waɗanda ba wai kawai suna ɗaukar bidiyo ba, har ma suna watsa abin da ke faruwa kai tsaye daga ɗakin otel ɗin.

Na sa ido kan ɗaya daga cikin waɗannan shafukan na tsawon watanni bakwai, inda na gano bidiyo daga kyamarori 54 daban-daban, kusan rabinsu suna aiki a kowane lokaci.

Wannan na nufin cewa, a cewar hasashen BBC bisa la'akari da yawan mutanen da ke kwana a otel a kullum, dubban baƙi na iya kasancewa an ɗauke su a bidiyo a cikin wannan lokaci inda mafi yawansu ba su da masaniyar cewa an taɓa ɗaukar su.

Eric, wanda ya fito daga Hong Kong, ya fara kallon irin waɗannan bidiyoyin da aka ɗauka a asirce tun yana matashi. Ya ce abin da ya ja hankalinsa shi ne yadda bidiyon ke kasancewa "na gaske".

"Abin da ya ja hankalina shi ne mutanen ba su san ana ɗaukar su ba, ba kamar yadda ake shiyawa ba wajen daukar bidiyon batsa na wasan kwaiwkayo ba," in ji Eric, wanda yanzu yake da shekara 30.

Amma daga baya ya ji raɗaɗin zama daya daga cikin wadanda aka dauki bidiyonsu lokacin da yake saduwa da burwarsa Emily a asirce.

Lokacin da ya sanar da Emily cewa an ɗauki bidiyon zaman su a otel, an gyara shi ya zama bidiyo mai tsawon awa ɗaya, sannan aka wallafa shi a Telegram, "da farko ta yi tunanin wasa nake yi. Amma bayan ta ga bidiyon da idonta, sai ta shiga yanayi na firgici da kunya."

Emily ta firgita matuƙa, tana tsoron ko abokan aikinta ko 'yan uwanta sun ga bidiyon.

Tsawon makonni, Eric da Emily ba su yi magana da junansu ba.

To, ta yaya wannan masana'anta, wadda ke cin gajiyar lokutan sirri na ma'aurata da na samari da budare ba tare da saninsu ba domin biyan bukatar masu kallo, ke aiki? Kuma su waye ke bayan ta?

Ɗaya daga cikin fitattun 'yan kasuwar wannan harkar da wakilin BBC ya ci karo da su shi ne wani da ake kira "AKA".

"Na nuna kaina a matsayin mai kallo, na biya kuɗi domin samun damar shiga ɗaya daga cikin shafukan watsa bidiyo kai tsaye da yake tallatawa, kan kuɗin rajista na wata-wata Yuan 450 kimanin dala 65 kenan." in ji wakilin BBC.

Da zarar na shiga, na samu zaɓin tashoshin bidiyo guda biyar, kowanne yana nuna ɗakunan otel da dama. Ana iya ganin ɗaki nan take da zarar baƙo ya kunna wutar lantarki ta hanyar saka katin ɗakin.

Haka kuma, akwai damar komawa baya a bidiyon kai tsaye daga farkonsa, da kuma sauke tsofaffin bidiyoyin da aka adana.

A manhajar Telegram, wadda aka haramta amfani da ita a China amma ake yawan amfani da ita wajen ayyukan da ba su halatta ba ne AKA yake tallata waɗannan bidiyoyin da ake watsawa kai tsaye.

Ɗaya daga cikin tashoshin Telegram ɗinsa ya kai mambobi kusan 10,000 a lokacin bincikenmu.

Haka kuma, ana samun tarin bidiyoyin da aka watsa kai tsaye da ya gyara a Telegram inda ake sayar da su kan kuɗi guda ɗaya.

A cikin kundin bidiyon, na ga bidiyo fiye da 6,000, tun daga shekarar 2017 in ji wakilin BBC.

Masu bibiyar AKA sun kasance suna ba da sharhi a sashen tattaunawar tashar Telegram yayin da suke kallon bidiyon batsar mutanen da ake dauka daga dakin otel da ba su san ana kallon su ba.

Mun samu damar gano ɗaya daga cikin kyamarorin da aka boye a wani ɗakin otel a birnin Zhengzhou da ke tsakiyar China, ta hanyar haɗa bayanai daga masu kallo da masu amfani da shafukan sada zumunta, da binciken da muka yi da kanmu.

Masu bincike a wurin sun samu damar shiga ɗakin, inda suka gano kyamarar. An ɓoye ta ne a cikin na'urar shan iska ta bango, sannan an haɗa ta da wutar lantarkin ginin.

An yi amfani da na'urar gano kyamarori da aka ɓoye, wadda ake siyarwa sosai a yanar gizo a matsayin "abu mai muhimmanci" ga baƙi a otel, amma ba ta ba da gargaɗi cewa ana kallon su a asirce ba.

Sai masu binciken suka kashe kyamarar, nan take labarin ya bazu da sauri a Telegram.

"An cire kyamarar, wani mai bibiyar shafin ya rubuta a babban tashar da AKA ke gudanarwa.

"Abin takaici ne ƙwarai, wannan ɗakin yana da mafi kyawun ingancin sauti!" AKA ya amsa a tattaunawar.

Amma bayan sa'o'i kaɗan, sai AKA ya sanar cewa an kunna wata kyamara a wani otel daban. Ya ce: "Wannan shi ne tashar watsawa bidiyoyin kai tsaye"

A bincikenmu na watanni 18, mun gano kimanin masu wannan sana'ar goma sha biyu kamar AKA.

Tattaunawarsu da masu bibiyar wadannan bidiyoyin batsar sun nuna cewa suna wa manyan mutane aiki ne na samar da bidiyo, wadanda suke kiran su "masu kyamara".

Wadannan mutane ne ke tsara saka kyamarorin a ɓoye da sarrafa tashoshin watsa bidiyo.

A yayin tattaunawa ta kai tsaye da AKA, ya nuna hoton saƙon wani da ya ce "masanin kyamara" ne, wanda aka rubuta da sunan "Brother Chun" cikin rashin sani inda nan take AKA ya gaggauta goge saƙon kuma ya ƙi tattaunawa kan sa, amma mun samu damar tuntuɓar "Brother Chun" kai tsaye.

Duk da shaidar da muke da shi cewa shi ne ya samar da tashar watsa bidiyo ga AKA, Brother Chun ya ce shi wakili ne kawai na sayarwa, amma ya amince cewa akwai wasu da ke sama da shi.

Abin da yake akwai shine cewa tabba ana samun kuɗi sosai a harkar. Bisa ga adadin mambobin tashar da kuɗin rajista, BBC ta kiyasta cewa AKA kadai ya samu ƙasa da Yuan 163,200 ($22,000, £16,300) tun Afrilu na bara.

A China, matsakaicin kudin shiga a shekara-shekara a bara ya kasance Yuan 43,377 ($6,200, £4,600), bisa ga hukumar kididdigar kasar.

A China akwai dokoki masu tsauri kan sayarwa da amfani da kyamarar leken asiri, amma bincike ya nuna cewa ana iya sayan kyamarar cikin sauƙi a babban kasuwar kayan lantarki ta Huaqiangbei.

Da wahala samun sahihan bayanai kan adadin mutanen da aka gurfanar a kotu kan aikata irin wannan laifi saboda hukumomin China sun rage bayyana bayanan shari'o'i n irin wadannan laifukan a shekarun baya.

Amma shari'o'in da aka samu sun ratsa duk fadin kasar, daga Jilin a arewa zuwa Guangdong a kudu.

Blue Li, daga ƙungiyar RainLily a Hong Kong, wadda ke taimakawa wadanda aka ɗauke su a asirce suna saduwa kuma aka wallafa bidiyoyin su a intanet ta ce bukatarsu tana ƙaruwa, amma aikin yana ƙara wahala.

Li ta ce: "Kamfanonin fasaha suna da babban nauyi wajen warware irin waɗannan matsaloli, domin manufofinsu ne ke tsara yadda abubuwan ke yaduwa."

BBC ta kai karar AKA da Brother Chun, da ƙungiyoyin da suke sarrafawa tare da wallafi bidiyoyin batsar mutanen da aka dauka a asirce, ga kamfanin Talegram amma ba ta dauki mataki ba.

Bayan kwanaki 10, Telegram ta ce: "Wallafa batsa ba tare da yarda mutanen da ke ciki ba haramun ne bisa sharuɗɗanmu" kuma suna duba da kuma karɓar rahotanni don share miliyoyin abubuwan da ke cutar da jama'a a kullum.

Mun sanar da AKA da Brother Chun cewa suna samun kuɗi daga cin zarafin baƙin otel, amma ba su mayar da martani ba.

Bayan sa'o'i kaɗan, shafin Telegram ɗinsu da ke tallata batsa ya bace, amma shafin intanet din AKA na wtasa bidiyoyin batsa kai tsaye da na biya kudi na shiga don bincike yana aiki.

Eric da Emily har yanzu suna cikin tsoro da firgici daga abin da ya faru.

Suna kasance suna saka hula su rufe fuskarsu idan za su fita a bainar jama'a don kada a gane su, kuma suna ƙoƙarin guje wa kwana a otel.

Eric ya daina amfani da Telegram don kallon batsa, amma wani lokaci yana shiga ya duba saboda tsoron bidiyonsu ya sake bayyana.