Halin da ƙasashen Afirka ke ciki a yunƙurin zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƙasashen Afirka za su ci gaba da fafatawa a wani zagayen na wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 - kuma wasu manya na cikin tsaka mai wuya.
Wasa shida ne ya rage daga cikin 10, kuma wasa biyun da za a yi a wannan watan zai iya fayyace makomar wasu daga cikin ƙasashen.
Tawaga tara da suka kammala a saman teburin rukunnansu ne za su wuce zuwa gasar kaitsaye, sai kuma huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na biyu da za su buga wasannin neman cike gurbi.
An sauya kociyoyi da dama a ɗan tsakanin nan a nahiyar, Najeriya da Senegal da Tunisia duka samu sababbin masu horarwa.
To me ya kamata 'yankallo su tsammata a wannan zagayen?
Najeriya na buƙatar nasara a gaggauce
Daga cikin manyan ƙasashe akwai Najeriya, wadda ke tsananin buƙatar cin wasa.
Ba ta ci wasa ko ɗaya ba a Rukunin C kuma akwai tazarar maki huɗu tsakaninta da Rwanda ta ɗaya.
Mai horarwa Eric Chelle ne ya karɓi aikin horar da tawagar ta Super Eagles a matsayin ɗan Afirka na farko wanda ba ɗan Najeriya ba da ya yi hakan.
Najeriya za ta ziyarci Rwanda ranar 21 ga watan nan, kafin ta karɓi baƙuncin Zimbabwe, kuma Chelle ya aminta cewa cin wasannin dole ne a gare su.
"Akwai matsi a harkar ƙwallon Afirka," kamar yadda ya faɗa wa BBC Sport Africa.
"Nakan ce lokaci ne babban maƙiyin kowane koci. Amma dai ina da ƙwarin gwiwa kuma na yarda da 'yanwasana."
Nijar na shirin ba da mamaki
Morocco ce Tawagar da ta fi kowacce matsayi a Afirka kuma ba ta yi rashin nasara ko canjaras ba a wasannin. Ita ce ta ɗaya da maki tara a Rukunin E.
A gefe guda kuma, Nijar da ke neman zuwa Kofin Duniya a karon farko, ita ce ke biye mata da maki shida, da Tanzania ma mai shida a mataki na uku.
Sai dai Nijar ɗin za ta karɓi baƙuncin Morocco ranar Juma'a, kuma idan har ta yi nasara to za ta bayar da mamaki mai yawa.
Ƙasar Eritrea ta fice daga wasannin tun kafin a fara bugawa, sai kuma a watan da ya gabata Fifa ta dakatar da Congo-Brazzaville daga shiga harkokin wasanni.
Yanzu an soke karawar da Congon za ta yi da Tanzania da Zambia a watan nan, kuma da wuya a iya sake tsara jadawalin a yanzu.
Yanzu za a jira Fifa ta yanke hukunci kan tawagar da za ta yi ta biyu a rukunin na E.
Masar ba matsala, amma sai sabbin koci sun dage

Asalin hoton, Getty Images
Masar ta fi kowace tawaga samun natsuwa a nahiya, inda ta bayar da tazarar maki huɗu a saman teburin Rukunin A.
Kyaftin Mohamed Salah ya ɗan samu hutu a ƙarshen zagayen wasannin neman shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta Afcon 2025, amma zai so ya ci gaba da ƙoƙarin da yake yi a Liverpool a wasan da za su buga da Habasha da Sierra Leone.
A gefe guda kuma, Sami Trabelsi ya sake karɓar aikin horar da Tunisia a karo na biyu kuma tawagar ta Carthage Eagles ce a saman teburin Rukunin H.
Gwarzuwar Afirka Ivory Coast ta bayar da tazarar maki ɗaya a Rukunin F, yayin da sabon kocin Kenya Benni McCarthy na neman kai ƙasar Kofin Duniya a karon farko idan ya rage tazarar da Ivory Coast ɗin ta ba shi.
A Rukunin D, Kamaru ta bai wa Cape Verde da Libya - wadda ta naɗa tsohon kocin Senegal Aliou Cisse mai horarwarta - tazarar maki ɗaya.
Kamaru na neman zuwa Kofin Duniya karo na tara.
Rukuni mai wuya
Yanzu haka, rukunin da ya fi kowanne matsatsi shi ne G, inda tawaga biyar na saman teburi ke da tazarar maki uku kacal a tsakaninsu.
Koci Vladimir Petkovic ya jagoranci Algeria samun gurbi a gasar Afcon 2025, amma za ta karɓi baƙuncin Mozambique da Botswana a watan Disamba.
Guinea da masu masaukin baƙin gasar Afcon 2027 Uganda na nan a laɓe suna jiran wani kuskure daga waɗannan tawagogin domin samun gurbi.
Ghana da Mali a Rukunin I
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ghana za ta yi bakin ƙoƙarinta don ganin ta manta da abin kunyar da ta yi a wasannin neman shiga gasar Afcon 2025 yayin karawarta da Chadi da kuma Madagascar.
Ita ce ta biyu a Rukunin I da maki tara, iri ɗaya da na Comoros ta ɗaya.
Sai dai za ta fuskanci sabon koci Corentin Martins na Madagascar, da kuma tsohon kocin Kamaru Rigobert Song a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wani sabon kocin shi ne Tom Saintfiet, wanda ke hanƙoron farfaɗo da tagomashin Mali a Rukunin I. Za ta iya rage tazarar maki huɗun da Comoros ta ba ta a saman teburi yayin da za su kara a wannan zagayen.
"Lamarinmu ba mai sauƙi ba ne, amma kuma ina da rukunin ƙwararrun 'yanwasa," kamar yadda Saintfiet ya shaida wa BBC.
Mali ba ta taɓa zuwa gasar Kofin Duniya ba, amma ganin yadda ta kammala zagayen farko na wasannin neman shiga Afcon 2025 ba tare da an doke ta ba, kocin na da ƙwarin gwiwa.
"Bayan wasa shida, nasara huɗu da canjaras biyu, lallai ina da ƙwarin gwiwa," in ji ɗan ƙasar Belgium ɗin.
Mamakin da Sudan ke bayarwa da kuma ƙoƙarin Senegal
Sabon kocin Senegal Pape Thiaw ne ke da alhakin kai tawagar Kofin Duniya bayan ya maye gurbin Aliou Cisse, wanda ya yi wa mataimaki.
Ba a ci su ba a wasannin neman zuwa gasar Afcon 2025.
"Pape ya aiki tare da Aliou, saboda haka muna da kyakkyawan tsarin cigaba," in ji tsohon tauraron ɗanwasanta El Hadji Diouf.
Sai dai kuma tana ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Sudan ta ɗaya wadda ta bai wa kowa mamaki. Kuma Nicolas Jackson da Iliman Ndiaye ba za su karawarsu da Sudan ɗin ba da kuma wasa da Togo.
Amma ko tsohon kocin Ghana Kwasi Appiah zai iya cigaba da samun nasarorin da ya faro tare da Sudan?











